Alamomin Ciwon Ulcer & Yadda Za’a Magance Shi

Karanta Cikakken Bayani Akan Alamomin Ciwon Ulcer & Yadda Za'a Magance Shi

 

 

Menene ciwon Ulcer?

Ciwon Olsa, ciwon gyambon ciki ne wanda ake kira ‘Ulcer’ a turance ce. Ciwon Ulcer yana faruwa ne lokacin da maɗaci (acid) na ciki ya cinye maka rufin ciki. Acid yana haifar da buɗaɗɗen raunuka ne wanda zai iya zubar da jini kuma ya haifar da ciwon gyambon ciki, Ulcer / Olsa. Kashi tamanin cikin ɗari na jama’a suna fama da wannan ciwon ta Olsa.

 

Gyambon ciki ’Peptic ulcer’ yana faruwa ne a lokacin da murfin ciki wanda ake kira ‘’mucous’, wanda ke bada kariya a can cikin ciki, idan karamin hanji wanda ake kira ‘duodenum’ ya lalace, yana barin maɗaci ’acid’ na ciki da enzymes masu narkewa su cinye cikin ciki tare da ganuwar karamin hanji duodenal.

 

Yadda Ake Gane Alamomin Ciwon Ulcer

Wasu cututtukan Ulcer / gyambon ciki ba sa nuna asalin bayyannar cututtuka inda ake kiran su ‘’silent ulcers’. Yadda ake gane asalin alamomin cutar Ulcer, sune a rubuce a kasa:

 

  • Kumburin ciki

  • Ciwon ciki mai kuna

  • Rashin narkewar abinci musanman irin abinci da ya kunshi maiko

  • Tashin zuciya

  • Yawan jin amai

  • Wani lokaci za’a iya fuskantar rashin jin dandano mai dadi a baki

 

 

Abubuwan da ke kawo ciwon ulcer

Abubuwa da dalilan da ke kawo ciwon gyambon ciki ‘Peptic ulcer’, suna da ɗan yawa, cikin wadannan dalilan da ke kawo ciwon Ulcer sun haɗa da:

 

  • Yawan Shan barasa / giya
  • Yawan yin amfani da magunguna irin su aspirin na yau da kullun, ibuprofen, naproxen, ko wasu magungunan anti-inflammatory marasa steroidal irin su NSAIDs, da ma sauran su
  • Yawan chin abinci mai sa tashin zuciya, kornafi da sauran su
  • Kwanciya da zarar aka gama cin abinci ba tare da motsa jiki ko da ɗan yawo ne
  • Yawan shan taba sigari ko tona ganyen taba
  • Tsananin kasancewa a halin rashin lafiya na dogon lokaci, musamman kamar kasancewa akan injin numfashi
  • Yawan kasancewa cikin damuwa
  • A wasu lokutan rashin motsa jiki zai iya haifar da ciwon gyambon ciki musamman ga mutane masu kiɓa

Dalilin da yasa aka dakatar da amfani da Indomie

 

Yadda Za’a Magance ciwon Ulcer cikin sauri

Hanyoyi da aka fi amfani da su a duk duniya wajen magance ciwon Olsa cikin sauri sune:

 

  • Yin amfani da magungunan rigakafi (antibiotics)
  • Yin amfani maganin da ake kira ‘Pantoprazole’
  • Yin amfani da maganin Antacids
  • Amfani da Acid blockers
  • Histamine receptor blockers
  • Sa’annan idan maras lafiyar yana shan giya ya guji shan giya kwata-kwata, bayan daina shan giya ciwon gyambon cikin zai sauka idan aka yi amfani da wasu magunguna kaɗan ciwon zai iya fita cikin sauri.
  • A yawan ta wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsabta
  • A yawan ta motsa jiki da zarar aka gama cin abinci

 

Lokacin Da Ya Dace A Kalli Likita

Ba lallai ba ne sai ciwo ya yi tsakani za’a kalli likita ba. Da zarar kuka ga alamun cututtuka da aka lissaf ta a sama a jikin ku, hanzarta zuwa domin ku Kalli Likitan ku.

Saboda zaku iya amfani da magungunan rage zafin ciwon da kwayoyi daga gida, sai dai hakan ba zai raba ku da ciwon ba, kuma ma yin haka zai iya haifar da c

iwon ya kara yin tsakani ko kuma ya haifar da wani sabon cuta.

 

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading