Tarihin Ali Nuhu Mohammed
Cikekken Tarihin Ali Nuhu Jarumin Kannywood
Wane ne Ali Nuhu?
Ali Nuhu Mohammed, wanda aka fi sani da Ali Nuhu, wanda jama’a ke masa lakabi da “Sarki Ali”, fitaccen jarumin fim din Hausa ne, kuma babban darecta (Ali Nuhu yafi ko wane ɗan fim din Hausa kuɗi da Sahara) an haife shi ne a ranar 15 ga watan Maris cikin shekarar alif 1974. A jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeria.A
Ali Nuhu kuma shahararren babban darakta ne a masana’antar Kannywood, kuma jarumin ya fito acikin fina-finan Hausa dama turanci wanda ake shirya wa a kudancin Najeriya. Ya fito a fina finai sama da fina finai ɗari biyar (500). Inda a yanzu haka Ali Nuhu Yana da shekaru kusan hamsin (51) a duniya.
Bayanan Ali Nuhu:
Asalin Suna: Ali Nuhu Mohammed
Wurin Haihuwa: Maiduguri Borno
Shekaru: 51
Sunan Baba: Nuhu Paloma
Sunan Mama: Fatima Karderam Digema
Asalin Jiha: Borno
Kasa: Nigeria
Sana’a: Actor, Director etc.
Addini: Islam
Yara: Uku (3)
Mata: Maimuna Abdulkadir
Instagram: @realalinuhu
Twitter: @alinuhu
Ilimi & Farkon Rayuwar Ali Nuhu
Duk da an haifi Ali Nuhu ne a jihar Borno, amma a jihar Kano ne ya girma kuma ya fara karatu daga primary. Ali Nuhu ya fara karatun sa na firamare ne a makarantar Riga Special Primary School dake kano, inda ya halarta daga shekarar alif 1979 zuwa shekarar alif 1985. daga nan yaci gaba da karatunsa na sakandare a bangaren Kasuwanci, a makarantar Gwamnati da ke Jihar Kano, daga shekarar alif 1986 zuwa shekarar alif 1988. Kuma ya samu shaidar kammala Sakandare a wajen.
Ali Nuhu ya kuma halarci Makarantar Sakandare ta Kimiyya da fasaha dake Dawakin Tofa daga shekarar alif 1989 zuwa 1991, inda anan ma ya sake samun shaidar kammala karatun na Sakandare.
Bayan kammala karatunsa na Sakandare, Jarumi Ali Nuhu ya ci gaba da karatu inda ya sami digiri nasa na farko a fannin fasahar Geography a Jami’ar Jos dake jihar plateau.
Bayan kammalawa ya tafi jihar Oyo Ibadan, dake kudancin Nigeria domin yin aikin bautar kasa. Sa’annan daga baya ya halarci Jami’ar Kudancin California na kasar Amurka inda ya yi karatu akan harkar shirya fina-finai da fasahar fina-finai na zamani. Sa’annan ya halarci jami’ar ISM Jami’ar Adonai American University, dake ƙasar Jamhuriyar Benin a 2018, inda ya fito da kwalin digiri na girmamawa.
Tarihin Fara Shirin Fim Ɗin Ali Nuhu
Jarumi Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne tun a shekarar alif 1999. Acikin wani fim mai suna “abin sirri ne”, a cikin wannan fim din Ali Nuhu ya taka rawar a zo gani, inda haka yasa aka fara sanin sa. Sa’annan sai fim da ya fito mai suna “Sangaya”, anan ma ya sake taka rawar gani wanda ya zamo sakamakon shaharar sa har izuwa yau, kuma fim din Sangaya fim ne wanda ya zama daya daga cikin fina-finan Hausa da suka fi samun kudi tare da burge jama’a a wancan lokacin.
Ali Nuhu ya yi hasashe a fina-finai da dama da suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda inda aka ba shi kyautar gwarzon dan wasan kwaikwayo a cikin rawar da ya taka a lokacin bayar da lambar yabo ta African Movie Academy Awards (2007). A shekarar 2019 Nuhu ya yi bikin cika shekaru 20 a harkar nishadantarwa inda ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500) daga lokacin farawar sa fim.
Aure Da Iyalan Ali Nuhu
Shahararren jarumi Ali Nuhu, magidanci ne mai farin ciki tare da iyalansa. Darekta Ali Nuhu Ya yi aure ne tun a shekarar 2003. Inda ya auri masoyi yar sa mai suna Maimuna Abdulkadir, kuma Allah ya albarka ce su zuri’a a cikin auren. Ali Nuhu yana daya daga cikin mazajen da suka yi sa’ar mata, inda matar sa Maimuna a wata hira da tayi da wasu manema labarai jarumar ta kwatanta mijinta a matsayin miji mai tunani kuma uba ne da zai iya zama misali mai kyau ga ’ya’yansa da suka haifa da masu tasowa.
Ya’yan Ali Nuhu
Ali Nuhu tare da matarsa Maimuna Abdulkadir, Allah ya albarka ce su da ya’ya uku, mata biyu da dansa namiji guda daya, haihuwar su na fari sun haifi ya ta mace mai suna Fatima, haihuwa na shine ɗan sa na miji mai suna Ahmad Ali Nuhu, kuma yana kama da Ali Nuhu sosai, sai haihuwar su ta karshe mai suna Nawahir.
Iyayen Ali Nuhu
Asalin mahaifin Ali Nuhu mai suna “Nuhu Paloma” ɗan asalin jihar Gombe ne, wanda aka haife sa a garin Balanga. Sa’annan mahaifiyar Ali Nuhu kuma yar asalin jihar Borno ce, inda aka haife ta a karamar hukumar Bama.
Duk da kasancewar mahaifin Ali Nuhu ɗan asalin jihar Gombe ne, mahaifiyar sa kuma yar jihar Borno, amma a jihar Borno ne aka haifi Ali Nuhu, sai dai kuma a jihar Kano ne ya karasa girman sa.
Jerin Fina Finan Ali Nuhu:
- Nasibi
- Mansoor
- Umarnin Uwa
- Gadan Ga
- Sabon Shafi
- Hawan Girma
- Khalid
- Maraichi
- Har Abada
- Qiyasi
- Shamsiyya
- Tawakkali
- Raliya
- Maryam Diyana
- Rawani
- Ban Ga Masoyi Ba
- Gidan Iko
- Zamba
- Kamilalla
- Nazari
- Garinmu da Zafi (Dawo-Dawo)
- Bilal
- Mujadala
- Sitanda
- Carbin Kwai
- Madubin Dubawa
- Wani Hanin
- Matan Gida
- Jinin Jikina
- Halacci
- ‘Yar Tasha
- Wutar Gaba
- Bani Bake
- Gamu Nan Dai
- Uba da ‘Da
- Baya da Kura
- Ba’asi
- Sallamar
- Bahaushiya
- Rariya
- Dangin Miji
- Ba Tabbas
- Mansoor
- Zuciya Da Hawaye
- Wacece Sarauniya
- Jarumta
- Mu’amalat
- Dattijo
- Shinaz
- Igiyar Zato
- So
- Kurman Allo
- Nasibi
- Hanyar Kano
- Sirrin Da Ke Raina
- Mai Dalilin Aure (Match Maker)
- Jinin Jiki Na
- Garbati
- ‘Ya daga Allah
- Idan Hakane
- Kanin Miji
- Mati da Lado
- Sai a Lahira
- Munafikin Mata
- Duniyar Nan
- So Aljannar Duniya
- Hujja
- Hakkin Miji
- Andamali
- Dakin Amarya
- Nadawo Gareki
- Wani Gari
- Kudi A Duhu
- Madubin Dubawa
- Gani Gaka
- Wani Hanin
- Kudi A Duhu
- Son Zuciya
- Dan Marayan Zaki
- Kara da
- Da Kishiyar Gida
- Haske
- Lamiraj
- Jarumin Maza
- Fari Da Baki
- Zuri’a
- Mai Jego
- Mai Farin Jini
- Halisa
- Matar Jami’a etc.
Jerin Fina Finan Ali Nuhu A Nollywood:
- One Lagos Night
- The Millions
- Merry Men: The Real Yoruba Demons
- Banana Island Ghost
- Ojukokoro: Greed
- The Wedding Ring
- Confusion Na Wa
- I Voted Now Wetin
- Last Flight to Abuja
- Memories of My Heart
Jaruman kannywood da suka fi dukiya
Fina Finan Ali Nuhu Da Ya Jagoranta:
- Mansoor
- Gamu Nan Dai
- ‘Yar Tasha
- Halacci
- Jinin Jiki N
- Ni Da Ke Mun Dace
- Kudi A Duhu
- Madubin Dubawa
- Bazan Barki Ba
- Farraqu
- Adamsy
- Ankwa
- Bana Bakwai
- Alaqa
- Izzar-so
- da daki soni
- lulu da andalu.
- akwai kura
- Uku sau uku.
Awards Awards Da Ali Nuhu Ya Lashe:
- Kyautar City People Entertainment Kannywood Face Nasara 2013
- Kyautar Gwarzon Jarumin Kannywood Ya Samu Nasara
- Kyaututtukan Jagoranci na 2014
- Kyautar Mafi kyawun Mawaƙin da Ya Samu 2014
- Kyautar Arewa Films ya lashe 2005
- Kyautar 3rd Africa Movie Academy Awards Kyautar Mafi kyawun Jarumi a 2007
- Kyautar Zulu African Film Academy Awards Best Actor a 2011
- Kyautar 9th Africa Movie Academy Awards Best Support Support Actor a 2013
- Kyautar Nigerian Entertainment Awards ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na 2013
- Kyautar Mafi kyawun Kyautar Nollywood Gwarzon Jarumi Jarumin (Hausa) s 2013
- Kyautar City People Entertainment Awards Mafi kyawun Jarumi a 2014
- Kyautar City People Entertainment Awards Kannywood Face a 2014
- Kyautar Arewa Music and Movie Awards Pride of Kannywood a 2014
- Kyautar Arewa Music and Movie Best Actor a 2014
- Kyautar Fina-Finan Nahiyar Afirka Na 19 Mafi Fitaccen Jarumin a 2015
- Kyautar Best Nollywood Awards Best Actor (Hausa) a 2015
- Kyautar Kannywood Gwarzon Jarumi ya Samu 2015
- Kyautar City People Entertainment Kannywood a 2015
- Kyautar Best Nollywood Awards Actor Hausa s 2016
- Kyautar Arewa Music and Movie Award a 2016
- Kyautar City People Entertainment Kannywood Face Nominated a shekarar 2016
- Kyautar Arewa Creative Industry, Entertainment Award a 2016
- Kyautar Wazobia FM’s COWA, Babban Mai Nishadantarwa a 2016
- Kyautar City People Entertainment Awards a 2017