Kasashen Afrika Masu Magana Da Yaren Turanci
Ƙasashen turanci a nahiyar Afirka
Afrika nahiya ce, da take gida ga mutane da suke bakaken fata. Mafi yawan kasashen Afrika, Kasashen turawa sun rene ta, a can lokacin baya, inda har yanzu akwai wasu ƙasashen da basu sami incin kansu.
Yawancin kasashen da suka yi wa Afrika mulkin mallaka, kasar Faransa ne da kasar Ingila, amma kasar Faransa ne akan gaba, da yawan kasashen da ta rena. In kasar Ingila ta zo na biyu, inda a yau zamu duba jerin kasashen afrika masu magana da yaren turanci.
Jerin Kasashen Afrika Masu Magana Da Yaren Turanci
Nigeria
Najeriya, da ke yankin Afrika ta yamma, ta kasance kasar baƙin fata da tafi magana da yaren turanci a duniya. Najeriya ta samu yencin kai daga turawan mulkin mallaka ne a shekarar 1960, inda yaren turanci take a matsayin harshen hukuma.
Ghana
Kasar Ghana dake yankin nahiyar Afirka ta yamma, na daya daga cikin jerin kasashen da Ingila ta rena, kuma masu amfani da yaren turanci. Ghana ta karɓi Ingilishi a matsayin harshen hukuma kasar ne, bayan samun ‘yancin kai a shekarar alif 1957. Ingilishi na da mahimmanci ga asalin ƙasar, yana aiki a matsayin harshen mulki, ilimi, da kuma na kafofin watsa labarai.
Karanta: jerin tarukan Nigeria
Kenya
Kasar Kenya, na yankin nahiyar Afirka ta gabas, inda kasar ta yi iyaka da tekun Indiya. Kasar Kenya ta hada iyakoki da kasashen kamar su, Somalia, Tanzania, Ethiopia da kasar Uganda. Kenya na daya daga cikin kasashen Afrika mai amfani da harshen turanci. Kasar Kenya gida ne ga wannan babban harshen Afrika, wato yaren ‘’Swahili’.
South Africa
Kasar Afirka ta Kudu, kasar ta haɗa iyaka da tekun Indiya. Kasar Afrika ta Kudu tana da tarihin wariyar launin fata lokaci mai tsawo, inda kasar yanzu haka take da harsunan hukuma guda 11, tare da yaren turanci aciki.
Kasar Afrika ta Kudu na harsuna kamar su Afrikaans da Zulu, kuma har zuwa yau kasar na ci gaba fuskantar bambance-bambancen harshe. Sa’annan kasar Afrika ta Kudu, gida ne ga wannan shahararren jarumin, wato Nelson Mandela.
Uganda
Kasar Uganda, da ke yankin nahiyar Afirka ta gabashi, harshen turanci shine harshen hukuma a kasar Uganda. Kasar Uganda ta haɗa iyaka ne da kasashe kamar su Kenya, Burundi, Ethiopia, démocratique du Congo, da kasar Sudan ta Kudu.
Zimbabwe
Kasar Zimbabwe, wacce a da ake kira Rhodesia a lokacin mulkin mallaka ta Birtaniyya, ta dauki turanci a matsayin harshen hukuma bayan samun ‘yancin kai. Turanci, tare da harsunan asali kamar su yaren Shona da Sindebele, kasar Zimbabwe ta haɗa iyaka da Zambia, Mozambique, da kasar Botswana.
Botswana
Kasar Botswana, a shekarun baya, ta kasance kasar da ke kan gaba wajen fama da yaɗuwar cutur HIV. Kasar Botswana tana amfani da harshen Ingilishi ne a matsayin harshen hukuma na kasar, tare da yaren Setswana. Kasar ta haɗa iyaka da Zimbabwe, Namibia, kasar Angola da sauran su.
Malawi
An kafa kasar Malawi ne a shekarar alif 1891. Kasar da ta yi iyaka da kasashe kamar su kasar Mozambique, Zimbabwe, Zambia da kasar Tanzania. A kasar Malawi yaren Ingilishi yana aiki ne a matsayin harshen koyarwa a makarantu kuma ana amfani da shi wajen sadarwar da harkar hukuma.
Lesotho
Kasar Lesotho, ƙaramar kasa ce, da ke makwabtaka da kasar Afrika ta Kudu, da kuma tekun Indiya. Yayin da Sesotho shine yaren ƙasar Lesotho, amma ana amfani da Ingilishi a cikin gwamnati da harkar ilimi.
Swaziland
Kasar Swaziland, na da tarihi sosai, kuma tana daya daga cikin kasashe masu amfani da harshen turanci, a lokacin mulkin mallaka sojojin Burtaniya ne da na kasar Holland, suka mallaki kasar.