Tarihin Stanley Nwabili, Golan Nigeria

Wane Ne Stanley Nwabili Golan Nigeria?

Mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle na kasar Nijeriya, wato Stanley Nwabali Wanda aka yi kuskure a rubuta sunan sa, aka rubuta shi a: Nwabili, kuma da sunan ne tauraron sa tazo haskawa aka san shi ayau.

 

Bayanan Stanley Nwabili:

Asalin Suna:      Stanley Bobo Nwabali

Shekarar Haihuwa: 10 June, 1996

Asalin Jiha:     Jihar Rivers

Addini: Kirista

Kabilar Nwabili: Igbo / Inyamuri

Asalin Kasa: Nigeria

Kungiya: Chippa United

Position: Mai tsaron raga

 

Wurin Haihuwar Stanley Nwabali

 

An haifi Stanley Nwabali ne a ranar 10 ga watan Yunin shekarar alif 1996, a yanzu haka mai tsaron gidan yana da shekaru ashirin da bakwai (27). An haifi Stanley Nwabili ne daga cikin dangin Ogba, da ke Port Harcourt cikin jihar Ribas dake yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Stanley Nwabali, kafin fara gasar cin kofin Afrika da ke gudana a kasar Ivory Coast, dayawa daga cikin magoya baya da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki daga cikin komitin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle, sun nuna rashin amincewarsu akan kasancewar Stanley Nwabali, wanda ba a san shi ba a matsayin mai tsaron gida na farko na Najeriya a gasar cin kofin Afrika AFCON Côté de voire 2024.

 

Sabun Kociyan Super Eagles ne wato, Jose Peseiro ne ya sauko dan wasan zuwa cikin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle, sa’annan ya jarraba bashi ya bashi dama. dan wasan mai shekaru 27, a shekarar da ta gabata ne a ɗan nuna irin hazakar da yake da shi ne, bayan da aka sanya shi cikin tawagar wucin gadi a shekarar da ta gabata.

Ya nuna ya nuna yana da korewa inda daga baya aka amince da Nwabali da wuri a lokacin da Najeriya ta kara da Guinea a wasan sada zumunta a ranar 8 ga watan Janairu, a birnin Abu Dhabi.

 

Stanley Nwabili, a lokacin buga wasan cin kofin Afrika da ya gudana a kasar Ivory Coast yayi abin a yaba masa sosai, bayan da ya yi fice da nuna natsuwa, kwarewa da kwazo acikin dukkani nin wasannin da ya zamo mai tsaron gida a gasar cin kofin AFCON 2024 a Ivory Coast. Stanley ya nuna kwarewa a dukkanin wasannin, musamman ma a wasan Najeriya da kasar South Africa, inda ya hana kwallo shiga ragar sa har sau biyu, wanda kuma shi ne ya ba kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle nasara.

 

Kuskuren Suna

Asalin sunan sa shi ne Nubali, inda aka yi kuskure aka saka Nwabili, amma kuskuren ya fara ne a lokacin da ɗan wasan yake kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars lokacin da aka yi masa rajista a matsayin Nwabili maimakon Nubali. Duk da a shekarar 2018 an samu an gyara sunan, amma har zuwa yanzu, ba’a daina kiran sa da sunan da aka yi kuskuren rubutawa ba.

 

Farawar Stanley Nwabali Kwallo

Wani abu mai ban sha’awa game da sabon mai tsaron ragar Nigeria wato Stanley Nwabali, shine ya fara buga kwallo ne a matsayin dan wasan gaba, mai zura kwallo. Ya fara buga kwallo ne a kungiyar kwallon kafa ta ‘Go Round’ da ke cikin ƙasar Najeriya, inda daga nan ne masu horar da matasa na kungiyar suka mayar Stanley Nwabali position zuwa mai tsaron gida.

Ɗan kwallon da yafi Messi and Ronaldo kuɗi 

Kungiyoyin Da Nwabili Ya Buga Wa Kwallo

Kamar yadda muka ce a sama, ɗan wasa Stanley Nwabali, kungiyar kwallon kafar sa na farko shine kungiyar kwallon kafa ta Go Round.

Kuma ya buga wasa wa kungiyoyin Najeriya har hudu, Nwabali ya taka leda a kungiyoyin Najeriya hudu ne daban-daban kafin ya koma Afirka ta Kudu. Cikin Kungiyoyin da Stanley Nwabili ya buga wa kwallo sun haɗa da:

Kungiyar kwallon kafa ta Go Round FC.

Ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta ta.

Bayan barin kungiyar Enyimba, Stanley Nwabali ya koma kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars.

Bayan shekara guda, ya sake tafiya kungiyar kwallon kafa Katsina United, ya taka rawar a zo a gani a kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, inda hazakar sa ya saka kungiyar kwallon ka

fa ta Chippa United suka dauko shi a shekarar 2022. Inda a yanzu haka Nwabili yana taka leda a kasar South Africa.

 

Karanta: jerin yan wasan ƙwallon Nigeria da suka fi dukiya 

Victor Osimhen yana mataki daya da Drogba a cewar Mourinho

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading