Tarihin Daddy Hikima Abale, Shekaru, Aure Da Ilimi

 

Tarihin Daddy Hikima

Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Suna, Daddy Hikima, Abale, sanda ko kuma Ojo. Shahararren jarumin fim ɗin Kannywood ne, wanda aka haife shi a ranar 16 ga watan March, 1991. Kuma yana daya daga cikin Jaruman da kasuwar sa take ci yanzu haka a masana’anar fina finai ta Kannywood.

Daddy Hikima ya kasance jarumi mafi saurin samun karɓuwa da shahara a masana’anar Kannywood, duk da cewa ya shigo harkar fim ɗin Hausa ne ta baya baya.

 

Bayanan Abale Daddy Hikima:

Ranar haihuwa: 16, March, 1991

Asalin suna: Adam Abdullahi Adam

Inkiya: Daddy Hikima, Abale Sanda da Ojo

Sunan baba: Abdullahi

Sunan mama: Under Research

Shekaru: 32

Sunan mata: Maryam Farouk Sale

Kasa: Nigeria

Asalin jiha: Jihar Kano

Sana’a: Actor, ma’aikacin asibiti

Kabila/yare: Hausa/Fulani

Addini: Islam

Lambar waya: under research

Email address: under research

 

 

Shekarun Daddy Hikima Abale:

An haifi Adam Abdullahi ko Daddy Hikima ne a ranar 16 ga watan Maris, a shekarar alif dubu daya da dari tara da chasai’in da daya (16-March-1991).

Inda a shekarar 2023. Abale Daddy Hikima yana da shekaru talatin da biyu (32) a duniya.

Kuma kamin jarumin ya fara samun karɓuwa a masana’anar fim ta Kannywood, ya dau lokaci yana a matsayin manajan wannan shahararriyar jarumar fim ɗin Hausa wato Aisha Aliyu Tsamiya.

 

Wurin haihuwar Daddy Hikima:

An haifi Adam Abdullahi Adam ne ko Daddy Hikima Abale a garin Sheka Bus Stop, dake karamar hukumar Kunbotso, daya daga cikin kananan hukumomi dake jihar Kano Nigeria.

Kuma a jihar ne ya taso ya yi karatun sa na Firamare da ma na Secondary school, har ma da karatun sa na koyan ilimin aikin likita, inda ya fito da takardar shaidar karatun Difloma.

Kuma jarumi Daddy Hikima Abale, ya yi magana game da irin kallon da wasu daga cikin jama’a ke masa a matsayin mai shaye shaye, yace a zahiri sam wannan ba halayyar sa bane, kawai taken fim ce.

 

Asalin sunan Abale Sanda ko Ojo:

Asalin sunan Daddy Hikima Abale ko kuma Sanda shi ne: Adam Abdullahi Adam.

Inda asalin sunan mahaifinsa kuma shi ne: Abdullahi Adam

Inda har yanzu aka gaza samun bayani akan sunan mahaifiyar Adam ko kuma Daddy Hikima Abale.

 

Tarihin Bash Neh Pha

 

Karatun Daddy Hikima Abale:

Abale ko Adam Abdullahi ya yi karatun sa na Firamare ne a makarantar, sheka primary school da ke garin Kano. Inda ya yi karatun sa na Sakandire a makarantar gwamnati (Government Day Secondary school dawakin Tofah) dake jihar Kano.

Inda daga baya Daddy Hikima Abale ya halarci kolejin koyan aikin likitanci, inda ya fito da shaidar karatun sa na Difloma a bangaren kiwon lafiya.

Kuma jarumi Daddy Hikima Abale, so dayewa a cikin fina finai da yake fitowa, yana yawan magana da nuna muhimmanci ilimi da tasirin ta ga rayuwar dan Adam.

 

Auren Daddy Hikima, Abale

Tarihin Abale Daddy Hikima
Abale

Daddy Hikima Abale ko Adam Abdullahia ya ango ce a shekarar 2023.

A ranar 27-01/ na shekarar 2023 ne Daddy Hikima ya auri masoyiyar rayuwar sa wato Maryam Farouk Sale.

Inda aka ɗaura auren a masallacin Uhud dake Unguwar Naibawa dake cikin ƙaramar hukumar Kumbotso, a jihar Kanon Nigeria.

Matar da jarumi Daddy Hikima ko Abale Sanda, ya aura wasu suna cewa wai Matar mai suna Maryam Farouk Sale, ta taɓa yin fim, inda wasu kuma daga wasu gefen suke musanta haka.

 

 

Jerin fina finan da Daddy Hikima ya fito aciki:

  • A Duniya
  • Haram
  • Sanda
  • Sayin daka
  • Indaranka
  • Iyalina
  • Uku sau uku
  • Makaryata
  • Gidan Dambe
  • Labarina
  • Na Ladidi
  • Yan Zamani
  • Muneer
  • Duniyar So
  • Da sauran su.

 

 

Jaruman Kannywood da suka nuna goyon baya ga Tinubu

Tarihin Aisha Binani

Jaruman Kannywood da suka fi kuɗi mata

 


Tambayoyi da jama’a ke yawan yi:

 

Abale Daddy Hikima yana da aure?

  • Daddy Hikima Abale yana da aure, A shekarar 2023. Inda ya auri masoyiyar sa mai suna Maryam Farouk Sale.

 

 

Mene ne Sunan matan Daddy Hikima Abale?

  • Sunan matar Daddy Hikima Abale shi ne, Maryam Farouk Sale.

 

Mene ne matakin Karatun Daddy Hikima Abale?

  • Matakin Karatun Daddy Hikima shi ne, diploma, a makarantar koyan aikin likitanci.

 

Nawa ne shekarun Daddy Hikima Abale?

  • Daddy Hikima Abale a shekarar 2023 yana da shekaru talatin da biyu (32) a duniya.

 

 

 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading