Dalilin Da Yasa Aka Kama Mr 442 A Kasar Niger

Dalilin da yasa aka kama mawaki mr 442 a jamhuriyyar Nijar

 

Mr 442 a kasar Niger
Mr 442

Laifin da Mr 442 ya aikata a kasar jamhuriyyar Niger har aka kama su, a shekarar da ta gabata ne shahararren mawakin Hausa hip-hop nan tare da darektan sa aka kama su a kasar Niger.

 

An kama Mr 442 ne tare da darektan sa mai suna Ola of Kano, Inda aka sare su, domin ci gaba da bincike akan laifin da ake zargin su akai.

 

Mene ne Dalilin Da Yasa Aka Kama Mr 442 A Kasar Niger?

 

Kamar yadda hukumomi kasar Niger suka tabbatar wa gidan rediyon (Freedom Radio), an kama mawaƙin ne tare da daraktan sa Ola of Kano, kan zargin kama su da takardun shaidar zama yan ƙasar Niger na bogi, wadda hakan ya saɓa wa dokar kasar.

 

Inda aka sare su domin ci gaba da gudanar da bincike akan haka. Sai dai daga baya akwai wani mutum da ya kara sanar wa gidan rediyon Freedom ɗin, cewa an kama su ne yayin da suke yunkurin yanka takardun (International passport).

 

mawakan Hausa hip-hop mata

 

Yayin hira da wasu manema labarai suka yi da shahararriyar mawakiyar Hausa hip-hop kuma abokiyar aikin Mr 442, wato Safara’u wacce ada take fitowa a cikin shirin fim din Kannywood mai suna ‘kwana chasa’in.’

 

Bayan tambayar ta da aka yi, akan ko ta san halin da abokin aikin ta Mr 442 yake ciki, ko kuma, Dalilin Da Yasa Aka Kama Mr 442 A Kasar Niger.

Safara’u ta sanar da cewa ta san halin da yake ciki, tace suna cikin koshin lafiya.

 

Tarihin Sadiq Saleh

 

 

 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading