Asalin Jihohin Ƴan Kabilar Yoruba A Nigeria

Jerin Jihohin kabilar Yoruba A Nigeria

Kabilar Yoruba sune kabila na biyu mafi girma bayan kabilar Hausa a Nigeria, mafi yawan yan kabilar Yoruba ana samun su ne a yankin Kudu maso yammaci sauran kuma a arewacin Nigeria.

Arewavoice.com
Yoruba

 Tarihin ƙabilar Yoruba

Yan Ƙabilar Yoruba kamar yadda tarihi ya nuna, kabilar sun yi ta rayuwa ne tun karni na bakwai 7 (7th century) da suka gabata, amma kabilar basu yi tasiri ba sai a karshe karshen karni na takwas 8, sakamakon wani babban masarautar yarabawa na Ile Ifi, masarautar da a lokacin yayi suna sosai.

Sarautar Ile Ife tana daya daga cikin masarauta mafi tasiri a farkon a karni na 7 zuwa ƙarni na 8, a fadin Afrika, Kamin zuwan karni na 11 yan kabilar Yoruba, sun mamaye yankin Kudancin Nigeria, kuma sun zama daya daga cikin manyan kabilu a Nigeria da ma Afrika.

 

Wasu jihohi ne asalin Jihohin Ƴan Kabilar Yoruba a Nigeria?

  • Oyo 
  • Ogun 
  • Lagos 
  • Osun 
  • Ondo 
  • Ekiti
  • Kogi
  • Kwara

 

Wadannan jihohin sune asalin Jihohin da za’a iya cewa gida ga yan kabilar Yoruba, amma akwai wasu jihohin dake arewacin Nigeriya inda ake samun yarabawa kamar su; Kwara da jihar Kogi.

 

Asalin Jihohin Ƴan Kabilar Yoruba?  Ga jerin jihohin da suke gida ne kabilar Yoruba a Nigeria:

 

Jihar Ekiti

Jihar Ekiti shine jiha na farko a jerin mu jihar na yankin kudu maso yammacin Nigeria, Ado Ekiti shine hedkwatar jihar. Jihar Ekiti tayi iyaka da jihar Kogi, Ondo da Osun. 

Jihar kuma ita ce jiha mafi karancin shekaru a yankin Kudu maso Yamma. Saboda an kafa jihar ne a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1996 tare da wasu jihohi biyar, a karkashin mulkin Sojojin kama-karya na marigayi Janar Sani Abacha. An saga  jihar ne daga tsohuwar jihar Ondo a shekarar 1996.

Jihohin kabilar Igbo 

Jihar Ibadan

 Jihar Oyo mai kananan hukumomi talatin da uku 33,  An kafa jihar ne daga yanki da ake kira, jihar Yamma a shekarar 1976 kuma da farko ta hada da jihar Osun. Jihar ta Oyo tayi iyaka da jihar kwara, Osun da kuma Ogun.

Wasu daga cikin manyan garuruwa a jihar Oyo sun hada da Ọyọ, Ogbomọsọ, Isẹyin, kishi, Okeho, Saki, Eruwa, Iroko, Lanlate, Oje-Owode, Sepeteri, Ilora, Awe, Ilero, Igbeti, Igboho da Igbo-Ora, Out. Kuma jihar Oyo gida ce ga jami’a ta farko a kasar Najeriya, Jami’ar Ibadan.  

 

LAGOS

Babban cibiyar kasuwanci a Nigeria da ma Afrika, wato Lagos wanda aka fi sani da Eko a harshen Yarbanci, Legas tana yankin kudu maso yammacin Nijeriya.

An ce jihar ita ce mafi yawan jama’a a Najeriya da kuma a Afirka. Legas babbar cibiyar hada-hadar kudi ce kuma ita ce ke da mafi girman GDP a Afirka. Inda ɗaya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa a Afirka yana Legas.

Wasu daga cikin wuraren da suka shahara a Legas sun hada da Lekki, Ikeja, Victoria Island, Lagos Island, Surulere, Ikorodu, Badagry, Epe, Ojo da Apapa.

 

JIHAR OGUN

An kirkiro jihar Ogun ne a shekarar 1976, jihar Ogun daya ne daga cikin jihohin Yarbawa. Taken jihar dai shi ne kofar shiga Najeriya domin ta yi iyaka da jamhuriyar Benin.

Kananan Hukumomi  a jihar ta Ogun sun hada da; Abeokuta.  Sauran garuruwan sun hada da Ijebu Ode, Ijebu Imusin, Sagamu, Ijebu Igbo, Ogere Remo, Iperu, Ilisan Remo, Ikenne, Ilaro, Ayetoro, Agbado, Akute da Ota.

 

  JIHAR ONDO

An kafa jihar Ondo ne daga jihar Yamma a shekarar 1976. kuma yawancin yan jihar  Yarabawa ne.  Sauran kabilu sun hada da; Akoko, Akure, Okitipupa, Ilaje, Ondo, da mutanen Owo, Ijaw da kuma mutanen Apoi da Arogbo suna zaune ne a yankunan bakin teku.

Jihar Ondo tayi iyaka ne da jihohi irinsu jihar Edo, jihar Kogi, jihar Ekiti, jihar Osun da jihar Lagos, kuma jihar ita ce tayi iyaka da ƙasar jamhuriyar Benin.

 

JIHAR OSUN

Jihar Osun ita ce babban birnin jihar Ile Ife, kuma ance ita ce mahaifar kabilar Yarbawa ma kanta, an kafa jihar Osun be a shekarar 1991 lokacin da aka sassaka ta daga wani bangare na tsohuwar jihar Oyo. 

Sunan jihar ya samo asali ne daga kogin Osun, maɓuɓɓugar ruwa da yarabawa suke  girmamawa. Jihar tana da kananan hukumomi 30, kuma Oshogbo ita ce babban birnin jihar.

Jerin Jihohin Arewa ta Yamma 

KWARA STATE

Duk da kasancewar jihar a yankin Arewacin Najeriya, jihar tana daya daga cikin jihohin yarabawa a Nijeriya. Jihar ta ƙunshi kabilu daban daban kama daga, Yarbawa, Nupe, Baripa da Fulani.  Duk da haka, Yarbawa ita ce kabila ta farko a jihar.

An kirkiro jihar Kwara ne a ranar 27 ga watan Mayun shekarar 1967, ta kunshi tsoffin lardunan Ilorin da Kabba na yankin Arewa a lokacin, da farko dai an sanya wa jihar sunan jihar ta yankin Yamma, inda daga baya aka canza shi zuwa “Kwara”. 

 Asalin jihohin yan kabilar Igbo

 

Jihar Kogi

Jihar kogi ita ta karshe a jerin mu na asalin Jihohin yan kabilar Yoruba a Nigeria, duk da kasancewar ta a yankin Arewa, jihar tana daya daga cikin jihohin yarabawa, kuma gida ga kabilar. Jihar kogi ta hada iyaka ne da jihohi irinsu, jihar Nassarawa, jihar Edo, jihar benue, jihar Ekiti, jihar kwara, da babbar Birni Abuja.

A jihar kogi ba dukan yankunan jihar ne ake iya samun yarabawa ba, ana iya samun yarabawa ne a cikin kananan hukumomi irinsu, Ijumu, Yagba West, Yagba East, Kabba/Bunu and Mopa da Moru.

Jerin Jihohin Arewa ta Tsakiya

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading