Jerin Kasashen Da Suka Fi Karfin Tattalin Arziki A Duniya

Wacce kasa ce tafi arziki a duniya?

Wasu kasashe suka fi kowane kasa dukiya a duniya? A wannan lokacin zamu duba jerin sunayen manyan kasashen duniya, da suka fi dukiya da arziki a duniya. kasashe irin su Kuwait, Qatar, San Marino da sauran su, suna daya daga cikin ƙananan kasashen da suka albarkatu da dukiya da albarkatun kasa, duk da kasancewarsu kasa wadanda basu da yawan al’umma. 

Jerin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya 2024

Kasashen Da Suka Fi Karfin Tattalin Arziki A Duniya
Kasashen Da Suka Fi Karfin Tattalin Arziki A Duniya

Kasashen Da Suka Fi Karfin Tattalin Arziki A Duniya sun hada da:

  1. United States – $18.23 Tn
  2. China – $11.23 Tn
  3. Japan – $4.95 Tn
  4. Germany – $3.43 Tn
  5. United Kingdom – $2.95 Tn
  6. France – $2.48 Tn
  7. India – $2.27 Tn
  8. Italy – $1.87 Tn
  9. Brazil – $1.81 Tn
  10. Canada – $1.54 Tn

 

Jerin kasashe da suka fi arziki a duniya bisa yawan al’umma 2023:

  • Ireland 
  • Luxembourg 
  • United Arab Emirates
  • Qatar 
  • Singapore 
  • Liechtenstein
  • Switzerland
  • America 
  • Norway 
  • San Marino 

 

  1. Ireland

Kasar Ireland ta kasance kasa da tafi kowane kasa dukiya a duniya idan aka yi la’akari da yawan al’ummar kasa. Ƙasar na da mazauna akalla miliyan 5 kawai, kuma ga tarun dukiya da albarkatun kasa da ma sauran kayayyakin more rayuwa, da na fasaha.

Hatta manyan kamfanonin Amurka da yawa irin su kamfanonin fasaha irin su Apple, Google, Microsoft, Meta da Pfizer da ma sauran su, sun ƙaura zuwa ƙasar Ireland ne domin cin gajiyar ƙarancin kuɗin haraji da suke saka wa kamfanoni a kasar.

2  Luxembourg

Duk da kasancewar kasar bata da yawan al’umma sosai, amma Luxembourg na daya daga cikin kasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya. KasarLuxembourg tana yankin tsakiyar tsakiyar Turai ne, inda ƙasar ke da sama da al’umma dubu 650,000 tana da wadataccen abin bayarwa, ga masu yawon bude ido da ‘yan ƙasa.  

3 United Arab Emirates (UAE)

Kasar United Arab Emirates Hadaddiyar Daular Larabawa, ita ce kasa mafi bunkasa yanzu haka a fadin duniya. Inda hanyoyin samun kuɗaɗen kasar ta hada cinikin dalu’u-lu’u, Noma, kamun kifi, sa’anan ga uwa uba rijiyoyin mai. waɗannan sun kasance jigon tattalin arziƙin wannan ƙasa ta.  Sannan an gano mai a shekarar alif 1950, inda daga nan kuma komai ya canza kasar ta fara bunkasa.

A yau, Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato United Emirates (UAE) al’ummar duniya daga sassa daban daban suna cin moriyar dukiyar kasar Dubai. Ga Gine-ginen gargajiya na Musulunci ya haɗu da wuraren kasuwanci masu ƙyalli na gwala-gwalai, ga gini mafi tsawo a duniya duk daga kasar. 

Jerin kasashen musulmai a duniya 

  1. Qatar

Kasar Qatar dake yankin Asia, ita ce kasa ta uku da tafi dukiya a duniya bisa yawan al’umma, kasar Qatar ta dogara ne da danyen mai

  1. Singapore

Kasar Singapore na daya daga cikin kasashe masu tarun dukiya, kuma kasa mafi bunkasa a fasahan ce. Kuma mutumin da ya fi kowa arziki a duniya yana zaune ne a kasar Singapore, wanda shi ne wanda ya kafa kamfanin kula da kayan aikin likita Mindray, Li Xiting, wanda aka kiyasta dukiyarsa ta kai dala biliyan 15.6.

5 Liechtenstein

Kasar Liechtenstein kasa ce da yawanci ba’a san da shi ba,sai dai kuma abin mamaki kasar na daya daga cikin kasashe masu tarin dukiya a duniya. Liechtenstein yana zaune a tsakanin kasar Ostiriya da Switzerland, kuma tsaunin Alps ne ke mamaye da ƙasar wanda ya sa ƙasar ta zama wurin shakatawa ga al’umma musamman ma lokacin sanyi.  

6 Switzerland

Kasar switzerland dake yankin Turai na daya daga cikin kasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.  Wannan kasa mai kimanin mutane sama da miliyan 8.8 tana bin bashin da yawa daga cikin dukiyarta ga ayyukan banki da inshora, yawon shakatawa, da kuma fitar da kayayyakin magunguna, duwatsu masu daraja, karafa masu daraja, da ma sauran kayayyakin fasaha.

  1. Amurka

Duk da kasancewar kasar Amurka a matsayin kasa mafi Ci Gaba a harkokin kimiyya da fasaha, amma hakan bai bata damar zama Kasa na farko a bangaren tattalin arziki ba. Kasar Amurka ita ce kasa ta biyu a jerin kasashen da suka fi arziki a duniya.

Shigowar Amurka da ci gaba da kasancewarta a cikin manyan 10 na faruwa ne saboda faduwar farashin makamashi da kashe kudade na jihohi. Faduwar farashin makamashi ya sa kasashe masu arzikin man fetur irin su kasar Qatar, Norway da Hadaddiyar Daular Larabawa, wato United Emirates, Saudi Arabia da ma sauran kasashe masu rijiyoyin mai. 

  1. Norway

 Kasar Norway da ke yankin Turai na daya daga cikin kasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya. Kasar ta fara gano kanta ne tun lokacin da aka gano manyan wuraren ajiyar teku a ƙarshen shekarar alif 1960s. 

Kasar Norway kuma na daya daga cikin kasashe masu rijiyoyin mai, saboda babbar hanyar samun tattalin arzikin kasar Norway ya kasance haɓaka danyen mai ne.

  1. San Marino

Kasar San Marino ita ce jamhuriya mafi tsufa a yankin Turai kuma ƙasa ta biyar mafi ƙaranci akan taswira.  Suna da yawan al’umma 34,000 ne kacal, amma kasar na cikin ƴan ƙasa mafi arziki a duniya. Duk da haka, San Marino yana aiki don daidaita dokokin kasafin kuɗi da ƙa’idodinta tare da na Tarayyar Turai ta (EU) da ƙa’idodin ƙasashen duniya. A yanzu haka dai darajar Dukiyar kasar San Marino ya Kaita zama a matsayi na goma a duniya.

Yan kwallon kafan Nigeria da suka fi dukiya

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading