Asalin Jihohin Kabilar Igbo A Nigeria

 

Igbo
Igbo

Kabilar Igbo ita ce kabila ta uku mafi girma a Nigeria, bayan Hausa da Yoruba, suna da kashi 18% cikin dari na jimilar yawan al’ummar kasar Nijeriya.

Mafi yawan mutanen kabilar Igbo suna daga yankin Kudancin Nigeria ne, yankin kudu maso yamma, sauran kuma suna ta kudu maso kudanci.

 

 Takaitaccen Tarihin kabilar Igbo

Akwai maganganu daban daban da ra’ayoyin jama’a kan asalin kabilar Igbo, inda yanzu za zamu duba cikin wadanda suka fi asali.

Wasu sun ce kabilar Igbo sun yi hijira ne daga yankin Gabas kuma suna ɗaya daga cikin ƙabilun kasar Isra’ila da suka taba ɓacewa kamar yadda ya ke a tarihi.

Wasu kuma sun ce sun taba yin hijira ne daga yammacin Afirka, Sai dai akwai shaidu kamar su bambancin harshe da ilimin kimiya na kayan tarihi da suka nuna cewa, kabilar Igbo sun yo hijira ne daga kasar Sudan daga wani tsohon birni mai 5 ‘Meroe’ a kusan AD350.

Mutanen Kabilar Igbo dai Mutane ne da suke masu dogaro dakan su, ta bangaren ayyukan hannu daban daban da kuma harkokin kasuwanci. Kuma za’a iya samun yan kabilar Igbo a kasashe irin su Cameroon da Equatorial Guinea.

 

Wasu jihohi ne asalin gida ga kabilar Igbo?

Abia, Akwa-Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross-River, Delta, Ebonyi, Enugu, Imo da Rivers.

 

Ga jerin sunayen; asalin Jihohin Kabilar Igbo a Nigeria.

 

 1. Abia – Umuahia

Jihar abia tana yankin kudu maso gabashin Nijeriya, jihar na da kananan hukumomi 17, mafi yawan al’ummar jihar yan kabilar Igbo ne.

 

2. Enugu – Enugu

Jihar Enugu mai kananan hukumomi 17, tana yankin kudu maso gabashin kasar nan, gida ne ga kabilar Igbo.

 

3. Anambra – Awka

Jihar Anambra tana yankin kudu maso gabashin Nijeriya, daya daga cikin jihohin Igbo, tana da kananan hukumomi 21.

 

4. Ebonyi – Abakaliki

Jihar Ebonyi tana yankin kudu maso gabashin Nijeriya, daya daga cikin jihohin Igbo, inda jihar take da kananan hukumomi 13.

 

 5. Imo – Owerri

Jihar Imo mai kananan hukumomi 27, tana yankin kudu maso gabashin Nijeriya mafi yawan al’ummar jihar yan kabilar Igbo suke.

 

Wadannan su ne asalin jihohin da za’a iya cewa jihohin Igbo kuma asalin gida ga kabilar, saboda yan kabilar Igbo ne zalla a jihohin.

 

Sanatoci sabbin fuska a majalisar Nigeria 2023

 

Wadannan jihohin kuma na kasa sune jihohin da yan kabilar Igbo ne suka fi yawa, amma a chakube suke da wasu kabilu.

Jerin sunayen jihohin Igbo da suke a chakube da wasu kabilu:

 

1. Akwa-Ibom – Uyo

Jihar Akwa-Ibom mai kananan hukumomi 31, tana yankin kudu maso kudanci kasar Nijeriya, daya daga cikin jihohin masu magana da Igbo.

 

2. Bayelsa – Yenagoa

Jihar Bayelsa tana da kananan hukumomi 8, da ke kudu maso kudancin Nijeriya, akwai yan kabilar Igbo a chakube da sauran kabilu.

 

3. Cross-River – Calabar

Jihar Cross River tana yankin kudu maso kudancin Nijeriya, ita ma jihar Igbo ta na chakube ne da wasu sauran yarurruka, jihar na da kananan hukumomi 18.

 

4. Delta – Asaba

Jihar Delta dake yankin kudu maso kudancin Nijeriya mai kananan hukumomi 25, ta na daya ne daga cikin jihohin dake yan kabilar Igbo.

 

5. Rivers – Port-harcourt

Jihar Rivers na yankin kudu maso kudanci, tana da kananan hukumomi 23, suna daya daga cikin jihohin da ake samun yan kabilar Igbo aciki.

 

6. Edo – Benin

Jihar Edo ita ma jiha ce da ke kudu maso kudancin Najeriya, jihar na da kananan hukumomi 18, ana samun yan kabilar Igbo a wasu garuruwan jihar.

 

Conclusion

 

Kabilar Igbo dai ana samun su ne a zone biyu cikin zone guda shida (6) da muke da ita a Nigeria.

wadannan zone guda biyun kuma sune, kudu maso gabas da kudu maso kudanci, amma kudu maso gabashi wurin suka fi yawa.

Me ra’ayinku akan: Asalin Jihohin Kabilar Igbo A Nigeria? Kuyi comments da shawarar ku akai.

 

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading