Jerin Jaruman Kannywood Da Suka Rasu 2023 – 2024
Kana Son sanin Jerin Jaruman Kannywood DaSuka Rasu a shekarar 2024?
Ga jerin mu na Jerin Jaruman Kannywood Da Suka Rasu daga shekarar 2023 zuwa 2024:
-
Hajiya Saratu Daso
Jumammiyar jarumar Kannywood ta Hausa wato Saratu, wacce aka fi sani da Hajiya Daso, Allah yayi mata rasuwa a cikin watan Ramadan, na cikin shekarar 2024.
-
Kamal Aboki
Jarumi Kamal aboki, dama yana daya ne daga cikin jaruman yankin Arewa mafi saurin tasowa da daukaka. Allah ya yi masa rasuwa ne a ranar 16 ga watan Janairu, cikin shekarar 2023. Ya rasu ne a hanyar sa ta zuwa jihar Borno, a hatsarin mota.
-
Abdulwahab Awarwasa
Jarumi Abdulwahab Awarwasa, shi ma da yana daya daga cikin jarumai, wadanda ake ji da su a yankin Arewacin Najeriya, kamin wanda ya bashi ran ya karbi abin sa. Allah ya yi masa rasuwa ne a ranar ashirin da uku (23) ga watan Janairu na cikin shekarar 2023. Kuma Abdulwahab Awarwasa, bayan kasancewar shi jarumi a kannywood shi furodusa ne.
Jaruman Kannywood Da Suka Fi Kuɗi 2024
-
Hajiya Binta Ola
Tsohuwar Jarumar Nollywood, wacce aka dama da ita tun farkon kafa masana’antar Kannywood wato Hajiya Binta Ola, ita ma Allah ya dauki rayuwar ta acikin shekarar 2023, inda ta rasu a ranar 4 ga watan Oktoba a shekarar 2023.
-
Kawu Mala Aminu
Daya daga cikin Jaruman Kannywood, mai suna Kawu Mala Aminu, ya rasu acikin shekarar 2023. Inda Allah ya dauki rayuwar sa, acikin watan Mayu. shekarar 2023, daya daga cikin tsofaffin jaruman kannywood.
-
Hannatu Umar
Jarumar Nollywood hannatu Umar wacce ta rasu a ranar ashirin 20 ga watan
Agusta na cikin shekarar 2023.