Jaruman Kannywood 13 Da Suka Nuna Goyon Bayansu Ga Tinubu

Jaruman Kannywood

Fitattun jaruman Kannywood da dama ne, suka nuna goyon baya wa Asiwaju, wanda aka fi sani da Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, a kamfen da aka yi a jihar Kano.

Dalilin gabatowar zaɓen shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023, ne ɗan takarar, wato Bola Ahmed Tinubu, ranakun talata da laraba ne, ya zayyana goyon bayan sa daga dukan jihohin yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Jaruman Kannywood suma sun hallaro domin nuna goyon bayan su, suma ga tsohon gwamnan jihar Lagos ɗin a zaben shekarar 2023.

Ɗan Takarar wato Bola Ahmed Tinubu, a filin kamfen din, ya yi alkawarin farfado da masana’antun da ke mutuwa a yankin, kuma tare da taimakawa wajen magance matsalar kananan yara da ake kira Almajiri idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben shugaban kasa a wata mai zuwa.

 

Kamfen ɗin an gudanar da shi ne a filin wasa na Sani Abacha, inda jaruman Kannywood ɗin suka burge magoya bayan jam’iyyar APC da kade-kade a yayin da suke neman goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, da sauran jama’ar APC.

Cikin jaruman da suka nuna goyon baya ga ɗan takarar shugaban kasar, sun hada da Ali Nuhu da Adam Zango, ga jerin sunayen su a kasa.

1. Ali Nuhu

Ali Nuhu, wanda aka fi sani da ‘Sarkin Kannywood’, shine ya yi dogon jawabi a madadin abokan aikinsa a wajen taron da aka yi a jihar Kano, Ali Nuhun yace “Gaskiya dai ba mu yi mamakin fitowar jama’a da yawa a yakin neman zabennan ba, saboda iran nasa rorin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu. Kuma Har ila yau, irin wadannan ayyukan ci gaba sun faru a jihar Legas lokacin da Ahmed Tinubu yake a matsayin gwamna.

Ali Nuhu ya kara da cewa “Mista Tinubu ya taimaka sosai wajen bunkasa Legas da daukacin yankin Kudu maso Yamma ba tare mai da hankali kan addini daya ba. Dalilin haka ne yasa muke kira ga jama’a da ku fito ku zabe shi da Nasir Gawuna da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a Kano. A ‘cewar Sarkin Kannywood’ Ali Nuhu.

2. Adam A. Zango

Adam A. Zango shima wani babba ne, a ma’aikatar ta Kannywood, Adam A Zango dai a farko ya nuna goyon baya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP), wato Rabiu Kwankwaso, inda daga baya ya koma goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, a lokacin yakin neman zaben a kano.

 

3. Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq

Shima jarumi Sadiq Sani Sadiq, ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a filin kamfen din.

 

4. Falalu Dorayi

Darakta Falalu Dorayi, shima ya halarci taron kamfen din, domin nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa.

 

5. Suleiman Bosho

Shima Sarkin bada dariya, wato Suleiman Bosho, ya nuna goyon bayansa ga Ahmed Tinubu, a filin taron kamfen din, wanda aka yi a jihar Kano.

 

6. Rabiu Daushe

Rabiu Daushe, shima shahararren jarumin barkwanci ne a masana’antar ta Kannywood, kuma an dade ana damawa da shi.

 

7. Dan Auta

Jarumi ɗan Auta, shima ya halarci taron kamfen din da aka yi a jihar Kano, shima ya nuna goyon bayansa ga Ahmed Tinubu.

 

8. Baba Ari

Baba Ari, shima tsohon jarumin barkwanci ne, da aka jima ana damawa da shi, a masana’antar Kannywood, kuma Har yanzu yana fitowa a wasu fina-finai.

 

9. Dangwari

Shima jarumi ɗan Gwari ya halarci taron kamfen din, tare da nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasar Najeriya, wato Alhaji Ahmed Bola Tinubu.

 

10. Fati Niger

Duk da kasancewar ta ba yar asalin ƙasar Nigeria bace, Fati Niger, na daya daga cikin jaruman da suke da magoya baya a ma’aikatar Film ta Kannywood.

 

11. Mustapha Nabriska

Shima jarumi mai suna Mustapha Nabriska, ya halarci taron kamfen din da aka yi a filin wasa na General Sani Abacha.

 

12. Dan Dolo

Tsohon jarumin shima ya halarci taron kamfen din, wato Ɗan Dolo, wanda shima tsohon jarumin barkwanci ne a masana’antar Kannywood.

Wanda ya fi kuɗi tsakanin Naziru da Rarara

13. Malam Kwaram

Jarumi Malam Kwaram, ya na cikin jaruman da suka fito don nuna goyon baya ga dan takarar shugaban kasa wato Alhaji Ahmed Bola Tinubu.

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading