Tarihin Auta Mg Boy Dana Farawar Sa Waka

Cikekken Tarihin Auta Mg Boy

 

 

Jarumi Abdulrahman Muhammad Garba wanda akafi sani da suna ‘auta mg boy’ shahararren mawakin hausa ne wanda aka haife shi a ranar daya ga watan Janairun shekarar alif 1993 (1 January 1993). Auta Mg Boy ya fara yin suna ne tun akan wakar sa mai suna baba “ayimini aure”, kuma wakar kusan ita ce silar samun daukakar sa.

Bayanan Auta MG Boy

Asalin Suna: Abdulrahman Muhammad Garba

Sunan Mama: ?

Sunan Baba: Muhammad Garba

Asalin jiha: Kaduna

Ranar Haihuwa: 1993

Shekaru: 30

Kabila: Hausa

Aure: ?

Inkiya: auta mg boy

Yara: ?

Addini: musulunci.

Sana’a: mawaki, marubucin waka.

Darajar Dukiya: 2 Million

 

Shekarun Auta Mg Boy

Haihuwar Auta Mg Boy; an haifi Auta Mg Boy ne a ranar daya ga watan Janairun shekarar alif dubu daya da dari tara da chasain da uku (1 Jan,1993). An haifi sa ne a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin tarayyar Nigeria, sa’anan ya girma ne a garin Zaria babban birnin jihar Kaduna.

 

Karatu / Ilimin Auta Mg Boy

Abdulrahman Muhammad Garba ‘Auta Mg Boy’, ya yi karatun sa ne a jihar sa ta haihuwa, wato jihar Kaduna, a garin Zaria. Sai kuma har zuwa yanzu ba’a iya samun isasshen bayanai akan makarantun da jarumi Auta Mg Boy ya halarta ba.

Karanta: tarihin Sadiq Saleh

Tarihin Fara Wakar Auta Mg Boy

Auta Mg Boy da jaruman kennywood
Auta Mg Boy

Mawakin Auta Mg Boy, kamar yadda ya bayyana wa wasu manema labarai, yace yana da ra’ayin yin waka ne tun yana karami. Sa’annan da aka masa tambaya akan wanda wakar sa take burge shi (Role model) cikin jaruman mawakan Hausa, mawaki Auta Mg Boy, ya ce mawaqi Umar M Sharif, shi mawakin da yake yawan sauraron wakokin sa.

Auta Mg Boy, ya sha matukar wahala kafin ya zama abin da ya zama a yau, Auta ya juma yana fafatawa ta hanyar auna basirarsa kafin, kafin aka sanshi ayau tun kan wakar sa mai suna baba “ayimini aure”, wanda ya jawo hankalin jama’a masoyan wakokin Hausa.

 

Sa’annan dalilin saurin samun karɓuwar Auta Mg Boy ita ce, hawan wakar sa da manyan jaruman kannywood ke yi, jarumai irin su Adam A Zango, da sauran manyan jarumai. Inda shi kansa Auta Mg Boy din yana hawa kan wasu daga cikin wakokin sa.

Karanta: wanda ya fi kudi tsakanin Rarara Da Naziru

Jerin Wakokin Auta Mg Boy

Jarumi Abdulrahman Muhammad Garba, wanda aka fi sani da Auta Mg Boy, tun kan wakar sa mafi farin jini da shahara da ya yi mai suna “baba ayimini aure” zuwa yanzu yayi wakoki da dama cikin wakokin sa sun haɗa da:

 

  • alhamdulilla
  • baba ayi mini aure
  • garinso
  • kina zuciyata
  • tuntibe
  • daga ke
  • yanzuma aka fara
  • soyayyace ta hadamu
  • duniyar so
  • bazan rabu dakeba
  • Mai farin jini
  • amana da amana
  • cikin zuciyata
  • mafar kina.
  • muda masoyanmu
  • ta bani
  • abun rabone
  • tunda inasonki
  • ki bani
  • nashiga so
  • masoyiya
  • kizo gareni
  • maryama
  • zuciya
  • labarina

 

Hadakar Waka Da Yayi Da Wasu Mawaka

Auta mg boy a kasancewar shi matashin mawaki mai farin jini, ya saka yayi wakoki a tare da manyan jaruman mawaka da dama kamarsu, cikin fitattun mawakan da Auta ya yi waka tare da su sun hada da:Adam A Zango, Auta Waziri, hamisu breaker, Kasheepu etc.

 

 

 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading