Tarihin Peter Obi, Shekaru, Yara Da Tarihin Siyasar Sa

Cikekken Tarihin Peter Gregory Obi

 

Wane ne Peter Obi?

Peter Gregory Obi wanda aka fi saninsa da suna Peter Obi. An haife shi ne a ranar 19 ga watan Yuli, cikin shekarar alif 1961. An haife sa ne a karamar hukumar Anaocha, Onitsha, dake jihar Anambra a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Peter Obi dai shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar Nigeria, daya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu shekarar 2023. Na uku bayan Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar.

Kuma Peter Obi ya taba zama gwamnan jihar Anambra har sau biyu a jere; daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2014.

 

Bayanan Peter Obi

Ranar haihuwa:19-7-1961

Ƙasa: Nigeria

Jiha: Anambra

Asalin suna: Peter Gregory

Wurin haihuwa: Anaocha, Onitsha

Shekaru: 61

Kabila/yare: Igbo

Sana’a: kasuwa/Siyasa

Sunan matar sa: Margaret Brownson

Ya’ya: Biyu (2)

Matakin Karatu: Digiri

Addini: Kirista

Lambar waya: under research

Email address: under research

 

Shekarun Peter Obi

An haifi Peter Obi ne a ranar 9 ga watan Yulin shekarar alif 1961, a garin Onitsha na jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya, dake makwabtaka da wasu jihohin yan kabilar Igbo. Inda a halin yanzu (2023) Peter Obi yana da shekaru 61 a duniya.

Kuma a lokacin da Peter Obi yake kan karagar mulkin gwamnatin jihar Anambra, ya kawo ma jihar ci gaba da dama kama daga buɗe harkokin kasuwanci wa jama’ar jihar, da kuma jan hankalin kamfanonin kasashen waje domin zuba jari a jihar.

 

Karatu/Ilimin Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasar Nigeria Peter Obi, ya yi karatun firamare a jihar sa ta Anambra, sa’annan ya halarci, Christ the King College, inda anan kuma ya yi karantun sa na sakandare.

Sa’annan kuma daga nan ya shiga jami’ar ilimi (University) da ke garin Nsukka a shekarar 1980, inda ya fito da kwalin digiri a ilmin Falsafa a shekarar 1984, sa’annan Peter Obi ya halarci Lagos Business School dake birnin Lagos.

Tarihin Aisha Binani

Peter Obi ya kuma halarci jami’ar Harvard Business School da ke birnin Massachusetts dake ƙasar Amurka, da kuma makarantar (London School of Economics) dake ƙasar Ingila, Business School dake ƙasar Columbia da ma sauran su, Peter Obi ya halarci wajajen ilimi da dama.

 

Wasu daga cikin makarantun da Peter Obi ya halarta sun hada da:

Makarantar, jami’ar Cambridge : George Business School.

Columbia Business School, New York, U.S.A. (Marketing Management)

Institute for management development, Switzerland, inda ya samu manyan takardun shedu.

London School of Economics (Financial Mgmt/Business Policy)

Kellogg Graduate School of Management, U.S.A. (Advanced Executive Program)

Oxford University: (Advanced Mgmt& Leadership Program)

 

Auren Peter Obi

A shekarar alif 1992, ne Mista Peter Obi yayi aure, inda ya auri masoyiyar sa mai suna: Margaret Brownson. Kuma Allah ya Albarka ce su da ya’ya biyu, mace daya da namiji daya.

Peter Obi yana yin iya bakin ƙoƙarinsa domin ya ɓoye abinda ya shafi rayuwar ahalin sa da daga idanun jama’a. A shekarar 2017, an yi ta yin rade-raden cewa auren su da Margaret na fuskantar kalubale.

Inda uwar gidan sa “Margaret” ta musanta jita-jitar da jama’a ke yi akan auren nasu, kuma tayi Allah wadai da masu irin wannan halin, inda ta kuma bayyana hakan a matsayin keta.

 

 

 Ƴaƴan Peter Obi

Peter Gregory Obi da matarsa Margaret Brownson, suna da yara biyu ne kacal a duniya, wadannan yaran sune:

Gabriella Nwamaka Frances Obi (diyar sa ta mace; farkon haihuwa).

Gregory Peter Oseloka Obi (ɗan sa na namiji; karami).

Dan Peter Obi wato, Gregory Oseloka ya kammala karatun sa na digiri a fannin ilimin Falsafa daga Jami’ar birnin Bristol dake ƙasar Ingila.

Inda ita kuma yar sa ta farko, Gabriella Nwamaka, ta riga ta yi aure, inda take auren wani hamshakin dan kasuwa, mai suna Chukwuma Okeke-Ojiudu, da ke zaune a Chicago.

 

Iyayen Peter Obi:

Kamin wannan lokaci dai, ba’a iya samun cikakken bayani akan iyayen Peter Obi ba, sai dai akwai tabbacin ya fito ne daga cikin dangin kabilar Igbo.

Kuma jihar sa ta Anambra tana daya daga cikin jihohin da suke gida ne ga yan kabilar Igbo a Nigeria.

Tarihin Dino Melaye

 

Yan’uwan Peter Obi

Peter Obi, shi ne haihuwa na biyu a wurin iyayensu da suka fito ciki daya, yana da yan uwa maza biyu da yan uwa mata biyu wanda suka fito ciki daya, duk da daya daga cikin su ta rasu a shekarar 2018 a jihar Enugu. sunayen yan uwansa da suke ciki daya sune:

Bibiana Adani (yar uwarsa mace, wacce ta rasu)

Fabian Chinwuba Obi (ɗan uwansa na miji)

Josephat Ndibe Obi (ɗan uwansa na miji)

Martina Obi (yar uwarsa ta mace)

 

 

 Sana’ar Peter Obi kafin Shiga siyasa

Kafin Peter Obi ya shigo harkar siyasa, dan kasuwa ne shi wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu a Nigeria dama wasu ƙasashen duniya.

Wasu daga cikin mukaman kasuwanci da Peter Obi ya rike kafin shiga harkar siyasa sun hada da:

Tsohon Shugaban ajiyar kudin ta: Fidelity Bank Plc.

Tsohon Shugaban: Guardian Express Mortgage Bank, Ltd.

Tsohon Shugaban: Future Views Securities, Ltd.

Tsohon Shugaban: Paymaster Nigeria Plc.

Tsohon Shugaban: Next International (Nigeria) Ltd

Tsohon Darakta a banki na: Guardian Bank Express .

Tsohon Darakta: Chams Nigeria Plc.

Tsohon Darakta: Emerging Capital Ltd

Tsohon Darakta: Card Center Plc.

Peter Obi ya rike mukamai irin wannan da dama a wanda wasu daga ciki ba’a samu cikakkun bayanai akan su ba.

 

Tarihin Siyasar Peter Obi

Tarihin Siyasar Peter Obi

Yanzu haka a Nigeria Peter Obi yana daya daga cikin shahararrun manyan yan siyasar kasar nan.

Kuma siyasar Obi ta fara fitowa fili ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra a shekarar 2003 karkashin jam’iyyar (APGA).

A shekarar 2006 hukumar zabe ta INEC ta ayyana abokin hamayyar Peter Obi, wato dan takarar jam’iyyar PDP mai suna “Chris Ngige” a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a shekarar.

Amma a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2006, kotun daukaka kara ta ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe a zaben gwamna a karkashin jam’iyyar (APGA).

Inda a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2006, aka rantsar da Peter Obi a matsayin gwamnan jihar Anambra, a karo na farko.

A ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2006 majalisar dokoki ta jihar Anambra ta tsige Peter Obi daga kujerar gwamna, inda mataimakiyarsa Virginia Etiaba ta maye gurbinsa a matsayin gwamna. Amma daga baya Obi ya kalubalanci dalilin da yasa ka aka tsige shi daga gwamnar jihar. Inda kotun daukaka karar ta dawo da shi kan kujerar gwamnan jihar a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2007.

Mista Obi ya sake barin kujerar gwamna a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, bayan zaben da aka gudanar, wanda dan takara na jam’iyyar (PDP) mai suna Andy Uba ya lashe zaben.

Amma daga baya Peter Obi ya koma kotu, da cewa bai kammala wa’adinsa cikekke ba, na tsawon shekaru hudu, lamarin da ya sa kotun koli ta Najeriya ta mai da hankali akan batun, inda daga baya kotun ta mayar da shi kan mulkin a ranar 14 ga watan Yunin, 2007.

Jerin sunayen Sanatoci 54 da suka lashe zabe a jam’iyyar APC

Mista Obi ya sake neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2010, inda a ranar bakwai 7 ga watan Fabrairu shekarar 2010, hukumar zabe ta (INEC) mai zaman kanta ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a karo na biyu.

Bayan kammala wa’adin mulki na biyu, Peter Obi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kuma a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 2018, aka ayyana shi a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, inda suka sha kayi a hannun Janar Muhammadu Buhari.

Kafin ya zo ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

 

Sayawar Peter Obi Takarar Shugaban kasa 2023

A ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2022, Mista Peter Obi ya ayyana aniyar sa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Amma daga baya ya canza sheka zuwa jam’iyyar Labour Party (LP).

Peter Obi ya zama dan takarar shugaban kasa daga karkashin jam’iyyar Labour Party (LP) bayan da wasu ‘yan takara irin su Pat Utomi, da sauran wasu yan takar karu suka janye masa gabanin zaben Firamare.

An gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023, Peter Obi ya zo na uku, bayan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC (wanda shi ne ya lashe zaben shugaban kasa).

 

Wane ne mataimakin Peter Obi? Kuma ɗan wane jiha ne?

Mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), wato Peter Obi shi ne, Yusuf Baba-Ahmed, wadda aka fi saninsa da “Datti”, wanda tsohon Sanata ne.

Yusuf Baba Ahmed Datti, Ɗan asalin jihar Kaduna ne, kuma tsohon Sanata ne, inda ya taba wakiltar jihar Kaduna a yankin mazabar Zaria daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2007.

Ahmed Datti dai daga farkon shekarar 2022, mafi yawan jama’a a fadin Nigeria suka sanshi, biyo bayan zaman sa matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, Inda suka yi nasarar zuwa na uku a zaben shekarar 2023.

 

 

Lambobin Yabo Da Ya Samu

Peter Obi mutum ne mai kokari da hazaka tun farkon tasowar sa, kuma yayi gwagwarmaya ta ɓangarori daban-daban a rayuwarsa.

Sakamakon irin nasarorin da Peter Obi ya samu a harkokin rayuwa, Obi ya samu lambobin yabo da girmamawa, lambobin yabon sun hada da:

Mutumin Igbo mafi fice a cikin shekaru goma na jaridar Champion a (2014)

Sun Newspaper’s Man of the Year (2007)

Man of the Year (2012)

Bill & Melinda Gates Foundation’s Best Performing Governor on Ezeife Leadership Foundation’s Leadership and Good Governance Award (2012)

Thisday Newspaper’s mafi kwazo cikin Gwamnoni a Nigeria, shekarar 2009.

This Day’s Governor of the Decade (2020)

Champion Newspaper’s Nigeria’s Most Trustworthy Governor (2009)

West Africa (ICT) Award for gwamna mafi kwazo a shekarar 2010.

Gidauniyar Zik Leadership Prize (2011) muryar Newspaper’s Award for Outstanding in Leadership and Governance a shekarar 2014.

Champion Newspaper’s Most Nigerian Library Association’s Golden Merit Award (2014)

Gidauniyar “Pontifical Equestrian Order of Saint Sylvester Pope and Martyr (2014)”

Shi ne Gwamna na farko da aka nada a matsayin mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman a lokacin da yake kan mulki.

Shi ne Gwamna na farko da aka nada a cikin kwamitin kula da tattalin arzikin shugaban kasa.

Shi ne Gwamna na farko da ya yi wa’adi na biyu a sabuwar jihar Anambra da tsohuwar jihar, wato kusan shekaru 40 da kafa jihar.

 

 

 

 

Tambayoyi da jama’a ke yawan yi

 

Mene Ne Kabilar/yaren Peter Obi?

  •  Peter Obi ɗan kabilar Igbo ne, daga jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya.

 

Mene ne shekarun Peter Obi?

  • A shekarar 2023, Peter Obi yana da shekaru 61 a duniya. An haife shi ne a 19-7-1961.

 

Mene Sunan matar peter Obi?

  • Sunan matar peter Obi shi ne, Margaret Brownson. Wanda ya aura a shekarar 1992.

 

Yaran peter Obi guda nawa ne?

  • Peter Obi yana da ya’ya guda biyu, na miji da ya mace.

 

Mene ne Sunan yaran peter Obi?

  • Sunayen ya’yan Peter Obi shi ne, Gabriella Nwamaka Frances Obi (diyar sa ta mace; farkon haihuwa).
  • Gregory Peter Oseloka Obi (ɗan sa na namiji; karami).

 

Ɗan wane jiha ne Peter Obi yake?

  • Peter Obi ɗan asalin jihar Anambra ne, daga karamar hukumar Onitsha.

 

Wane ne mataimakin Peter Obi a 2023?

  • Yusuf Ahmed Datti, shi ne wanda mataimakin ɗan takarar shugaban kasa Peter Obi a karkashin jam’iyyar Labour Party.

 

 

 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading