Jerin Jihohin Arewa Maso Gabas

Sunayen Jerin Jihohin Arewa Maso Gabas

Jerin sunayen jihohin arewa maso gabashin Nijeriya. Kamar yadda yake a rubuce kasar Nigeria na da yankuna shida (6) ne. Inda waɗan nan yankuna suka haɗa da; kudu maso gabas, kudu maso yammaci da kudu maso kudu. A yankin Arewa kuwa akwai Arewa maso Gabas, Arewa maso yammaci, da Arewa ta Tsakiya. Inda a wannan lokaci zamu lissafo muku Jerin Sunayen Jihohin Arewa Maso gabashin Nijeriya.

 

Jerin Jihohin Arewa Ta Gabas Sune:

 

 

 Adamawa – Yola

Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya. an kirkiri jihar Adamawa ne cikin shekarar alif 1991. An kirkiri Jihar Taraba ne daga jikin Gongola a shekarar 1991. Inda mayar wa Jihar Gongola suna zuwa jihar Adamawa. Sunan babbar birnin Adamawa ne Yola. Kuma jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowace jiha yawan kabilu a Nigeria.

Tarihin  Arewa 

 Bauchi – Bauchi

Bauchi da ke yankin a arewa ta gabas mai makwabtaka da jihar plateau. An kafa jihar Bauchi ne a cikin watan Fabrairun na shekarar alif 1976. Inda aka kirkiro jihar daga jikin tsohuwar jihar Arewa maso Gabas. Kuma jihar a can lokacin baya jihar na cikin jihar Gombe ne na yanzu.

 

 Borno – Maiduguri

Jihar Borno ta hada iyaka da jihohin Adamawa, jihar Gombe, jihar Yobe da kuma ƙasar Kamaru. An kirkiri jihar Borno ne a ranar 3 ga Fabrairun na shekarar alif 1976 daga tsohon yankin Arewa maso Gabas. Kuma galibin al’ummar jihar Borno yan kabilar Kanuri ne. Kuma sunan babbar birnin jihar ita ce Maiduguri.

Jerin Jihohin Arewa ta yamma 

 Gombe – Gombe

Jihar Gombe sunan babban birnin jihar ma Gombe ne. Jihar na yankin arewa maso gabashin Najeriya ne. An kirkiri jihar Gombe ita ma daga cikin jihar Bauchi, a ranar 1 ga watan Oktoba, cikin shekarar alif 1996.

Jerin sunayen manyan jihohin arewa 

 State – Jalingo

Jihar Taraba da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wanda aka kirkiro ta daga tsohuwar jihar a ranar 27 ga watan Agustan shekarar alif 1991. Daga tsohuwar jihar Gongola a wancan lokaci, Gongola da ta kunshi jihar Adamawa da Taraba a can baya.

Jihohin yan kabilar Inyamurai 

  Yobe – Damaturu

Jihar Yobe na yankin arewa maso gabashin Najeriya, an kirkiro jihar Yobe ne daga jikin tsohuwar jihar Borno a ranar 27 ga watan Agustan, shekarar alif 1991. sunan babbar birnin jihar Yobe shine Damaturu. Jihar Yobe ta hada iyaka ne da Jihohin Gombe, Bauchi, Borno da jihar Jigawa.

Jerin Jihohin Yan kabilar Yoruba 

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading