Wa Yafi Kuɗi Tsakanin Rarara Da Naziru Sarkin Waka?
Mawaka na daya daga cikin wadanda ke taka rawar gani a bangaren siyasar kasar Nijeriya, ta hanyar tallata ɗan takara.
Kana so ka san wanda yafi kuɗi tsakanin rarara da naziru Sarkin Waka? Wannan batun jama’a suna yawan tambaya akai tun a farkon farkon shekarar 2023. Mawaki Dauda Kahutu Rara Ra Da Mawaki Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka, shahararrun mawaka ne wanda a shekarun baya bayan nan suka sami kansu, suna kwatanta kansu a bangaren da suka shafi tarun dukiya da kuma na gwaninta a waka. Tambayar anan shi ne wa yafi kuɗi tsakanin Dauda Kahutu Rara Ra Da Naziru M Ahmad Sarkin waka?
Wanda Ya Fi Kuɗi Tsakanin Dauda Kahutu Rara Ra Da Naziru M Ahmad Sarkin Waka
Kamin mu ci gaba da bambance wanda ya fi dukiya tsakanin Naziru Da Rara Ra, zamu fara ne da duba takaitaccen bayanai akan mawakan biyu wato: Naziru M Ahmad Sarkin Waka da Dauda Kahutu Rara.
Wane ne Naziru Sarkin Waka?
Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin waka, shahararren mawaki ne wanda ke waka da Yaren Hausa, Sarki Naziru ya shahara ne wurin yi wa manyan sarakuna, yan gidan sarauta da manyan attajirai waka, kamin daga baya ya fara yi wa manyan yan siyasa waka.
Naziru Sarkin waka yana daya daga cikin manyan mawakan da Arewacin Nijeriya suka taba samu a tarihi, saboda irin baiwar da Allah ya yi masa na iya tsara waka, kuma yana da nasa salo daban daga sauran mawaka na Hausa.
Nawa ne darajar dukiyar Naziru Sarkin waka?
Allah ne kaɗai ya fi sanin ko nawa ne yawan kuɗi ko darajar dukiyar da Naziru Sarkin waka yake da shi.
Naziru Sarkin waka idan aka zo bangaren kuɗi ko dukiya ma, yana daya daga cikin wadanda suka mallaki dukiya da kudade sosai a yankin Arewacin Najeriya.
Sarki Naziru ya juma yana waka, kuma ya juma da samun kuɗi, kuma ma a shekarar da ta gabata ya samu kuɗi sosai akan wata wakar da ya yi wa ɗan takara Atiku Abubakar, wakar mai suna ‘sai mun bata wuta’ wakar ta samu karɓuwa sosai.
Naziru Sarkin waka a shekarar 2023, darajar kuɗin da ya mallaka a kayyade ya kai sama da N700 million.
Wane ne Dauda Kahuta Rarara?
Dauda Kahuta Rarara wanda aka fi sani da Rarara kawai, daya ne daga cikin shahararrun mawaka a yankin Arewacin Najeriya, kuma shahararre a Nigeria bangaren wakar siyasa.
Sanatocin da suka lashe zabe karkashin jam’iyyar PDP
Rarara ya samu daukaka ne a shekarar 2015, lokacin da ya yi ta wakoki wa ɗan takara shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ya lashe zabe, ya sake lashewa kuma a shekarar 2019.
Nawa ne darajar Dukiyar da Rarara ya mallaka?
Nan ma Dauda Kahuta Rarara yana daya daga cikin wadanda suka mallaki kudade a cikin manyan mawakan yankin Arewacin Nijeriya. Kuma ya samu kuɗi da kyaututtuka sosai daga Bola Tinubu kan wakar da ya yi masa mai suna, ‘jagaba shine gaba’.
Allah ne kaɗai yasan ko nawa ne darajar kuɗin da Rarara ya mallaka.
Ganin irin rawar da Rarara ya yi ta takawa a bangaren siyasa wurin tallata yan takara har sukai ga chima burin su na cin mulki, darajar dukiyar da Rarara ya mallaka a shekarar 2023 a kayyade ya kai sama da N900 million.
Conclusion
Bayan dubawa da muka yi tsakanin Naziru Sarkin waka da Dauda Kahuta Rarara, zamu ga cewa shi Naziru Sarkin waka ya juma da ya soma waka kuma ya riga Rarara jumawa a harkar da ma yin suna, ya kuma ya riga Rarara samun kuɗi.
Shi kuma Rarara duka duka a shekarar 2015. ne ya yi suna har aka sanshi a Nigeriya, sai dai nasarar da ya samu na tallata yan takarkaru har sukai ga lashe zabe, shine ya ajiye shi a gaban Naziru Sarkin waka.
Tarihin Sadiq Saleh
Wa yafi kuɗi tsakanin Naziru Sarkin waka da Rarara?
Babu shakka Rarara shine wadda yafi kuɗi, saboda irin nasarar da ya samu, idan muka duba ko da bangaren wakokin sa da yayi wa siyasa, yan takarar shugaban kasa sau uku a jere kuma dukan su suka sami nasarar lashe zaɓuɓɓu kan su. Misali tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Rara Ra ya Tallata shi kuma ya yi nasara a jere. Ya taimaka wa tsohon gwamnan jihar Kano Ganduje ya yi nasara sau biyu. Sa’annan kuma ga shugaban kasa dake kan mulki a yanzu Tinubu.
Karanta: jerin jaruman Kannywood Da suka fi kuɗi
Jaruman Kannywood mata, da suka fi kuɗi