Tarihin Aisha Binani, Karatu, Aiki, Da Aure

Wacece Aisha Binani?

Aishatu Dahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Suna Binani, shahararriyar yar siyasa ce, yar kasuwa, injiniya kuma yar takarar gwamna. yanzu haka Aisha Binani tana matsayin sanata, inda take wakiltar Adamawa ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC.

Aisha Binani ta soma harkar siyasa ne shekaru kaɗan kamin tauraron ta ya zo ya haska a shekarar 2011, inda ta lashe zabe a matsayin mai wakiltar Yola north,Yola south da Girei a majalisar wakilai.

 

 Shekarun Aisha Binani

An haifi Aishatu Dahiru Binani ne a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 1971. Inda yanzu haka tana Shekaru 52 a duniya, a matsayin sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, kuma yar takarar gwamna a zaben shekarar 2023, wanda zai gudana a ranar 18 ga watan Maris kamar yadda hukumar INEC ta bayyana.

 

 Karatun Aisha Binani

A bangaren Ilimi kuma Aisha Dahiru Ahmed Binani, ta yi makarantar na sakandire ne a makarantar gwamnati dake Yola, sa’annan ta yi karatun ta na Difloma a Federal Polytechnic da ke garin Mubi, cikin jihar Adamawa. Daga baya kuma Aisha Binani ta fita kasar Ingila inda ta yi karatu a fannin Injiniyan Lantarki a Jami’ar Southampton, da ke kasar England.

 Auren Aisha Binani

Aishatu Binani, tana da aure kuma har da yara, Aisha Binani matar aure ce. Ta auri Farfesa Ahmed Modibbo, kuma babban Farfesa ne na jami’a. Kuma Allah ya Albarka ce su da ya’ya biyar (5) kamar yadda wasu manyan gidan jarida suka tabbatar.

 

Sana’o’in Aishatu Binani

Kafin Aisha Binani ta shiga harkar siyasa, ta kasance yar kasuwa, kuma ta taɓa zama shugaba a kamfanin kasuwanci, wacce ta kafa nata nakanta mai suna, Binani Nigeria Limited.

Ta kafa wannan kamfani ni domin haɓaka tattalin arziki na yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, wanda yan kungiyar Boko Haram suka nakasa, kuma wannan kamfani ya taimaka wa jama’a da dama a yankunan Arewaci dama sauran Najeriya.

 

Tarihin Siyasar Aisha Binani

Binani

Bayan ci gaba da Aisha Binani ta yi ta ɓangarorin kasuwanci, Binani ta shigo harkar siyasa, da kaɗan kaɗan, bayan samun kwarewa a siyasa ta yanke shawarar sayawa takara.

Jerin sanatocin Nigeria 

A shekarar 2011, Aisha Binani ta saya takara a matsayin mai wakiltar (house of representatives) mazabar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei, a majalisar tarayya Abuja, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sa’annan a shekarar 2018, sanata Aishatu Ahmed ta dauki fom din tsayawa takarar sanatan Najeriya karkashin jam’iyyar APC. Ta yi nasara a zaben fidda gwani na Firamare, sa’annan a shekarar 2019, Aisha Binani ta lashe zaben Sanata yankin Adamawa ta tsakiya, mai kananan hukumomi 19.

A shekarar 2022, Aishatu Binani ta sayi fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC. Ta yi nasara a kan dukkan nin yan takarar gwamna a zaben Firamare a karkashin jam’iyyar APC.

Aisha Binani ta yi nasarar lashe zaben Firamare ne da kuri’u 430, mai bin ta a baya wato Nuhu Ribadu, yana da 288, na uku kuma tsohon gwamna Bindow Jibrilla, da kuri’u 103, sauran biyun kuma 94 da 39.

Yanzu haka dai Aisha Ahmed Binani, tana jiran zuwan lokacin zabe ne, wanda zai gudana a ranar 18 ga watan Maris kamar yadda hukumar INEC ta bayyana.

 

Karanta: sabbin fuska a majalisar dokoki 2023

Iyayen Aisha Binani

Aishatu Dahiru Ahmed Binani, wacce haifar Jihar Adamawa ne, Iyayenta, sunayen iyayen ta na asali.

Asalin sunan mahaifnta: Alhaji Dahiru Ahmed.

Mahaifiyar Aisha Binani ta rasu a ranar 10 ga Disamba, shekarar 2020,

Asalin sunan mahaifiyar ta: marigayiya Hajiya Aishatu Utiya.

 

 

Aisha Binani tana da aure?

Kwarai kuwa Aisha Binani tana da aure kuma har da yara. Sunan mijinta, Ahmed Modibbo.

 

Mene ne Sunan mijin Aisha Binani?

Sunan mijin Aisha Binani shine, Ahmed Modibbo, wanda kuma professor ne.

 

Aisha Binani tana da yara?

A cewar wasu manyan tashoshin da zumunta, Aisha Binani tana da yara har guda biyar, tsakanin ta da mijinta Ahmed Modibbo.

 

Aisha Binani biography

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading