Tarihin Bash Neh Pha, Shekaru Karatu Da Sana’a
Wane ne Bash Neh Pha?
Matashin mawaki na Hausa hip-hop wato Bashir Halliru Alhassan, wadda aka fi saninsa da suna ‘Bash Neh Pha’ an haife shi ne a ranar daya ga watan December, a shekarar 1998. Shahararren mawaki ne, daga jihar Plateau dake yankin Arewacin Nigeria, Bash Neh Pha, mawaki ne mafi Sa’a, ta yadda ya shahara cikin karamin lokaci, duk da bai jima da fara waka ba.
Bayanan Bash Neh Pha
Ranar haihuwa: 1998
Asalin suna: Bashir
Sunan baba: Halliru Alhassan
Sunan mama: Under Research
Sunan ɗan uwa: Under Research
Sunan budurwa: Under Research
Sunan kasar sa: Nigeria
Sana’ar Bash: Waka Da Makanike
Aure: Babu Aure
Yaren Bash Neh: Hausa
Addini : Musulunci
Shekarun Bash Neh Pha
An haifi Bash Neh Pha, a garin Jos jihar Plateau, a ranar daya ga watan Disamba cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin, (1st, December 1998). Inda yake da shekaru (25) a shekarar 2023.
ya soma harkar waka ne a yaren Hausa da turanci, har aka fara sanin sa a kananan lungu na cikin garin Jos. Bayan yan wasu watanni da fara wakoki mawakin ya ɗauka ka, tare da samun magoya baya, daga wurin jama’a a yankin Arewacin Nigeria, da ma Afrika.
Karatun Bash Neh Pha
Bashir Alhassan “Bash Neh Pha“, ya yi karatun sa na primary da Secondary school ne a garin haihuwar sa, wato garin Jos na jihar Plateau, inda a watannin baya kamar yadda ya sanar wa wasu Manema labarai, cewa har yanzu yana makaranta, domin ci gaba da karatu.
Tarihin Fara Wakar Bash Neh Pha
Bash Neh Pha, ya fara wakoki ne a cikin garin sa na Jos, kuma ya fara koyan wakoki ne tun yana karami, kamin daga bisani atake ya samu daukaka bayan da wani gidan talabijin mai suna ‘Africa Magic TV’ ta dauki nauyin nuna gasar mawaka na (Rap Battle), Bash Neh Pha ya samu damar fafatawa aciki, inda ya bada jama’a mamaki tare da burge dubban masoya nishadi, Wanda gidauniyar ‘Giant Entertainers Lagos’ suka dauki nauyinsa.
Bash Neh Pha Yayi wasan ne Tare Da wasu manyan mawakan Arewa, da ma wasu manyan mawakan Nigeria. Kuma wakar sa da yayi da B.O.C Madaki, mai suna “Bullet” Ya Sa mutane da dama su mika mika wuya ga bajintar sa.
Sakamakon irin rawar da Bash Neh Pha ya taka, hakan ya jawo hankalin kamfanin FKG (FASHION KILLERS GROUP). kamfanin FKG, kamfani ce ta mai da hankali kan harkokin kayakin sakawa na zamani. inda a shekarar 2018, Bash Neh Pha ya rattaba hannu a karkashin kamfanin ta FKG.
Nasarorin da Bash Neh, ya samu
Mawaki Bash Neh Pha, ya samu nasarori da dama tun farawar sa waka, ya fara samun nasara ne tun lokacin da gidan talabijin mai suna ‘Africa Magic TV Rap Battle, wanda wasu manyan masoya nishadi suka dauki nauyin sa, daga jihar Lagos.
inda bidiyon ya wanzu zuwa gidajen talabijin na yankin Afirka daban daban.
Kwararrun mawakan Hausa hip-hop
Kamar yadda mawakin ya sanar wa manema labarai, ya ce ya fara yin wakoki ne tun yana ɗan karamin yaro. Waƙoƙin Bash Neh Pha galibi suna ɗaukar saƙonni masu kyau, kuma Kalmominsa suna sa mutane suyi tunani da kuma yaba baiwar sa. Wakokinsa Kamar “Matsalar Arewa” Wanda ke Magana game da yadda rayuwar al’ummar Arewa ta ke cikin wani hali, yana kokarin tunatar da shugabannin yankin Arewa ne, da su kara himma.
Wakar sa mai lakabin ‘mama’ ya jawo hankalin jama’a, bayan fitar da bidiyon wakar mai suna “Mama”, wasu daga cikin Jama’a sun fara tambayar me yasa yake maida hankali akan uwa Kadai, mahaifi fa? ya amsa wa jama’a ne ta 360hausa.com.ng
Inda kai tsaye ya amsa wa jama’a kan al’amarin da cewa “baban sa Allah ya yi masa rasuwa, (Ya Mutu), amma kuma kullum yana yi masa Addu’a amma a Keɓe.
Ya kara da cewa dukan iyaye sun cancanci girmamawa da soyayya.
Wakokin Bash Neh Pha:
- Inaso Ki Sanni
- Matsalar Arewa
- Kune Mata
- Bullet
- Duniya
- Mune
- Mama
- Jos Kawai
- Zaman Lafiya
- Yar Alhaji
- Yarinya
- Gareji
- Mai Taimako
- Birthday
- Mutuwa, etc.
-
Bash Neh Pha, Lambar waya Da Shafukan Sa Da Zumunta:
Facebook Page: @BashNehPha
Instagram: @bash___neh___pha
Twitter: @BashNeh
Phone Numer: Under Research
Email: Under Research
Me Ra’ayin ku akan Tarihin Bash Neh Pha, Shekaru Karatu Da Sana’a?
Thanks For Reading ❤️
Gwamnoni masu kananan shekaru a Nigeria
Mene ne Asalin sunan Bash Neh Pha?
Asalin sunan sa Bashir ne.
Bash Neh Pha yana da aure?
Mawaki Bash Neh Pha bayi da Aure tukuna.