Jerin Kasashen Musulmi 30 A Duniya

Kasashen Musulmi nawa ne a duniya?

 

A yadda masana sukayi bincike, Musulunci ta kasance addini ta biyu (2) a duniya yanzu haka, kuma babu addinin da ta kai addinin Islama saurin bunkasa a duniya. Mun yi bincike akan kasashen da mafi yawan al’ummar ta Musulmai ne, kamar yadda yake a kasa.

Jerin kasashen musulmai a duniya :

 

1. Maldives

Kasar Maldives, ta kasance kasa ce wadda za’a iya cewa kasar Musulmai ne zalla, saboda kashi dari bisa dari na al’ummar wannan kasar Musulmai ne. Inda yanzu haka wannan dalilin ne yasa ka wannan kasar yakasance kasa ta farko a duniya idan ana maganar kasar Musulmai zalla.


2. Mauritania

Kasar Mauritius ta kasance Jamhuriyar Musulunci, kuma shi ya ba ta damar zama a matsayin na biyu a duniya idan ana maganar kasar Musulmai zalla. inda ita ma Mauritius, kashi 100 na al’ummar kasar Musulmai ne.

 3. Afghanistan

Kasar Afghanistan, ta kasance kasa ce da ke yankin Asiya, inda wannan kasar ta haɗa iyaka da kasashe da suka haɗa da, Pakistan, Saudi Arabia, India da sauran ƙasashen yankin Asiya.

Inda Kashi 99.8 na al’ummar Afghanistan musulmi ne.

  4. Tunisia

Kasar Tunisia, ta kasance kasa da ke yankin Afrika ta gabas. Inda Kashi 99.8 na al’ummar kasar Tunisia musulmi ne. Kuma addini musulunci, ita ce addini kasar a bayyane.

5. Iran

Kashi 99.8 cikin ɗari na al’ummar kasar Iran Musulmai ne. inda yawan ci musulman kasar masu bin akidar shi’a ne. Kasar Iran na yankin Asiya ne, inda kasar ta haɗa iyaka da kasashe kamar su Iraqi, Saudiyya, Afghanistan da sauran su.

6. Iraq

Kasar Iraki na yankin Asiya ne. Inda jama’ar kasar Iraki kashi chasa’in (99) cikin ɗari (100) musulmi ne zalla. Inda kasar ta haɗa iyaka da Iran, Turkiyya, kasa mai sarki, wato Saudiya, da kasar Masar.

7. Morocco

Kasar Maroko ta kasance ne a yankin yammacin Afirka, inda kasar ta haɗa iyaka da kasashe kamar su; Tunisia, Algeriya, Western Sahara, kuma ruwa ne kawai ya raba ta da kasar da kasar Spain. Kashi 99 cikin 100 na Al’ummar kasar Maroko Musulmai ne.

8. Yemen

kasar Yemen ya kasance kasa ne da ke yankin Asiya, mai makwabtaka da kasar Saudiyya, kasar Oman kuma ruwa shi ya raba ta da kasar Ethiopia. Inda al’ummar kasar Yemen kashi 99 cikin dari Musulmai ne zalla.

9. Somalia

Kasar Somaliya, kashi 99.9 na al’ummar kasar Somaliyana Musulmai ne. Kasar da ke Afrika, mai makwabtaka da da kasashe kamar su Ethiopia, kasar Kenya da yankin Asiya. Inda yawan ci musulman suna bin akidar Sunnah ne.

 10. Turkey

Kashi 99.2 na Al’ummar kasar Turkiyya masu yawan jama’a sama da 83,156,000 lMusulmai ne. Kuma yawan ci masu bin akidar Sunnah ne. Kasar Turkiyya ta haɗa iyaka da kasashe kamar su: Greece, Syria da sauran su.

11. Algeria

Kasar Algeriya mai yawan jama’a sama da miliyan 43,905,000. kashi 98.5 daga ciki masu bin musulunci ne. Inda yawan ci musulman kasar Algeriya masu bin akidar Sunnah ne.

12. Niger

Kasar jamhuriyar Nijar, dake yankin Afrika ta yamma, mai makwabtaka da kasar Nigeriya, kasar Mali, kasar Libya, kasar Chadi da Algeriya. Kasar jamhuriyar Nijar al’ummar Nijar Kashi 98.5 na jama’ar kasar Musulmai ne.

 13. Kasa mai sarki: SAUDI ARABIA

Kasa mai sarki wato Saudiya, Kashi 98.7 cikin dari na al’ummar kasar Saudiyya, Musulmai ne. Kuma bangaren Sunnah na Musulmai shi ne addinin gwamnati a hukumance, a kasar.

Kasa mai sarki wato Saudiya, ta kasance a yankin Asiya ne inda ta haɗa iyaka da kasashe kamar su Iraqi, Iran, Oman da kasar Yemen.

 14. Sudan

Al’ummar kasar Sudan kashi 97 cikin ɗari ne Musulmai. Kuma yawan ci masu bin akidar Sunnah ne.

15. Azerbaijan

Mai yawan jama’a sama da mutane miliyan 10,067,000. Al’ummar Azarbaijan dai kashi 96.9 cikin dari Musulmai ne. Yawan ci masu bin akidar (Shiites) ne.

16. Djibouti

Kashi 97.9 na cikin al’ummar kasar mai yawan jama’a sama da 988,000, Musulmai ne. Inda kasar Djibouti ta haɗa iyaka da kasashe da suka haɗa da Ethiopia, Eritrea da ma sauran su.

17. Tajikistan

Yawan al’ummar Tajikistan kashi 96.7 cikin ɗari Musulmai ne. Inda kasar take da yawan jama’a da ta kai sama da miliyan 9,314,000.

18. Libya

Kasar Libya na da yawan jama’a da ta kai sama da miliyan 6,871,000. Inda kashi 96.6 al’ummar kasar Libya Musulmai ne. Kasar da ke yankin Afrika.

  19. Pakistan

Al’ummar kasar Pakistan kashi 96.4 cikin ɗari Musulmai. Inda kasar ta haɗa iyaka da kasashe da suka haɗa da kasar India, kasar Afghanistan, kasar Nepal, kasar Oman, kasar Iran da sauran wasu ƙasashe.

 20. Senegal

Kasar Senegal da ke yankin Afrika ta yamma ta kasance kasa mai yawan jama’a sama da miliyan 16,706,000. Inda Al’ummar kasar Senegal kashi 95.9 cikin 100 Musulmai ne zalla.

21.  Kosovo

Kasar Kosovo Kashi 95.7 na al’ummar Kosovo Musulmai ne. Inda ƙasar Kosovo take da yawan jama’a sama da miliyan 1,800,000.

22. Uzbekistan

Al’ummar Uzbekistan kashi 96.5 cikin ɗari Musulmai. Kasar Uzbekistan tana yankin Asiya ne, kuma ana samun masu bin akidoji daban daban a wannan kasar.

23. Jordan

Kasar Jordan mai yawan jama’a da ta kai sama da mutane miliyan 10,758,000 a duniya. Al’ummar kasar Jordan kashi 93.8 cikin ɗari Musulmai. Kasar Jordan ta haɗa iyaka da kasashe kamar su Israel, Lebanon, Iran da ma sauran su.

24. Gambia

Kasar na yankin Afirka ne, mai makwabtaka da kasashe kamar su kasar Senegal da kasar Guinea-bissau. Kasar Gambia na da yawan jama’a da ta kai sama da mutane miliyan 2,417,000.

 25. Mali

Kasar Mali mai yawan jama’a da ta kai sama da mutane miliyan 20,251,000. Inda al’ummar kasar kashi 95 cikin 100 Musulmai ne. Kasar tana nan ne a yankin Afrika.

26. Palestine

Kasar Palastinu tana da yawan jama’a da ta kai sama da mutane miliyan 5,201,100. Kasar ta haɗa iyaka da kasashe kamar su kasar Jordan, kasar Isra’ila da kasar Masar.

27. Bangladesh

Kasar Bangladesh ta kasance daya daga cikin kasashen musulmai a duniya. Inda kasar ke da yawan jama’a da ta kai sama da mutane miliyan 165,000,000. Inda Kashi 92% cikin ɗari na al’ummar kasar Musulmai ne.

28. Mayotte

Kasar mayotte tana daya daga cikin kasashen musulmai a duniya. Inda kasar ke da yawan jama’a da ta kai sama da mutane dubu dari 283,000 a duniya.

29. Western Sahara

Kasar Western Sahara, na yankin Afirka ne, inda kasar ta haɗa iyaka da kasashe kamar su Mauritius da wasu ƙasashen Larabawa da ke yankin Afrika.

30. Comoros

Kasar Comoros na da yawan jama’a da ta kai sama da mutane dubu 870,000.A duniya, inda yawan ci musulman kasar masu bin akidar Sunnah ne.

 

Jerin Jihohin Arewa Ta Tsakiya 

Asalin Jihohin yan kabilar Igbo

Jerin manyan jihohin arewa 

Tarihin Arewa 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading