Tarihin Dino Melaye Shekaru, Sana’a, Ilimi Da Yara

 

An haifi Dino Melaye ne a ranar bakwai ga watan Janairu, cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da saba’in da hudu, (7 Jan,1974). A jihar Kano dake yankin Arewa maso yammacin Nigeria. Yana da shekaru 49 a duniya ya zuwa shekarar 2023.

Dino Malaye tsohon sanata ne kuma tsohon dan majalisar wakilai a majalisar dokokin Najeriya.

Sanata Dino Melaye ya fito ne daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu dake jihar Kogi, a yankin Arewa maso Tsakiya. Dino Malaye babu shakka yana daya daga cikin manyan yan siyasar Najeriya mafi tasiri, da shahara a yau.

 

Bayanan Dino Melaye

Asalin suna:      Dino Daniel Melaye

Sana’a:       ɗan siyasa

Shekaru:     01/01/1974 Shekaru 49

Jinsi:        Na miji

Kasa:          Nigeria

Aure:           Gauro

W/haihuwa:     Kano, Nigeria

Yara:            Isra’ila, Joshua, Oluwajomiloju

Karatu:       Digiri, Ahmadu Bello University

 

Shekarun Dino Melaye

Sanata Dino Melaye an haife shi ne a ranar bakwai ga watan Janairu, cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da saba’in da hudu, (7 Jan,1974). A jihar Kano dake yankin Arewa maso yammacin Nigeria. Kamar yadda yake a shekarar 2023 Yana da shekaru 49 a duniya.

 

 Karatun Dino Malaye

Sanata Dino Melaye kana ganin sa zaka gane cewa ya samu karatu daidai gwargwado. Inda

ya halarci makarantar Abdulaziz Attah Memorial College da ke garin Okene, sannan ya yi karatun sa na sakandire, kafin ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna, inda ya yi karatun sa na digiri a fannin labarin kasa (geography) a shekarar 2000.

 

 

 Sana’ar Dino Malaye

Sanata Dino Melaye, kafin ya shigo harkar siyasa ya samu kwarewa ta wasu ɓangarori na rayuwa, kuma yana daya daga cikin yan siyasa mafi yawan dukiya a Nigeria, kuma ba’a iya Siyasa kaɗai ya tara dukiyar ba.

A hirar da Sen. Dino Malaye, yayi da gidan rediyon BBC pidgin, Dino ya sanar dasu ta inda yawanci ya samu kuɗi, ya ce ya tara kuɗi ne, a wani babban kamfanin hannun jari na kasar waje mai suna; McDonald’s, kamfanin dake ƙasar Amurika.

A lokacin da ya ke makaranta, ya kasance fitaccen mamba a na kungiyar dalibai ta kasa (NANS). ya fara ne a matsayinsa na jagoran kungiyar dalibai a zamaninsa na jami’a, daga baya, ya zama Sakatare-Janar na Majalisar Matasan Afirka da Majalisar Matasa ta +Commonwealth). Ayyukan da ya yi a matsayinsa na shugaban dalibai ya sa shugaban Najeriya na lokacin, Olusegun Obasanjo, ya nada shi shugaban kwamitin ba shugaban kasa shawara kan matasa.

 

Aure Da Ya’yan Dino

Sanata Dino ya taba auren Tokunbo Melaye, wanda daga baya ta shigar da kara kotu, inda ta ke zargin shi sanata Dino da cin zarafinta a gidan ta na aure.

 

An kuma ruwaito cewa Dino Melaye sun haifi yaro tare da jarumar fina-finan Nollywood wacce ake shirya wa cikin harshen turanci da kuma yarabanci a kudancin Najeriya, wato Bisi Ibidapo Obe, ya kuma haifu tare da Alero Falope, wacce yar aikin gidan ne.

Wasu daga cikin ya’yan Dino Melaye sun hada da:

Isra’ila

Joshua

Oluwajomiloju

 

Tarihin Siyasar Dino Malaye

Sanata Dino Melaye a yau, yana daya daga cikin manyan yan siyasa a tarihin Nijeriya, ya fara da shiga harkar siyasa ne, lokacin bangaranci, a shekarar 2007 lokacin da aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta kasa domin wakiltar mazabar Kabba/Ijumu a karkashin jam’iyyar PDP.

Ya sha kaye a zaben wa’adi na biyu, wadda hukumar INEC, tace a sake maimaita wa matsayin dan majalisar wakilai amma daga baya ya koma majalisa a matsayin Sanata a shekarar 2015, Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma.

 

Tarihin Aisha Binani

 

Karo na biyu an sake zabansa a majalisar dattawa a shekarar 2019, amma daga baya hukuncin kotu ta dakatar shi, inda ta soke tsarin zabensa tare da ayyana sake tsayawa takara.

Bayan sake sabon zaben abokin hamayyar sa wato Sanata Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC shi ne ya lashe zaben kuma aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, wanda hakan ya sa Dino ya rasa kujerarsa a zauren majalisa.

 

 

Iyaye Da Ƴan Uwansa

Iyayen Sanata Dino Melaye, sunan baban Dino Melaye shi ne, Mr. Jonah Eseyin.

Sunan mama: Dino, Mrs. Comfort Melaye. Amma a shekarar 2019, ne mahaifiyar sa ta rasu.

Sen. Dino Melaye, yana daya daga cikin ya’ya shida da iyayen sa suka haifa a duniya.

ya taso ne tare da sauran yan uwansa su shida wadda a ciki, akwai Samuel, Shade, da Elizabeth Melaye, wadannan su ne yan uwansa na jini.

 

Sanatoci da suka lashe zabe karkashin jam’iyyar APC

 

Motocin Dino Melaye

Dino ya shahara da sha’awar sayan motoci zamani, kekuna da kuma gidaje, inda yake da motoci akalla ashirin da biyar (25).

Wasu daga cikin motocin da Sanata Dino Melaye ya mallaka sun hada da:

Bugatti Veyron (N616 million), Lamborghini Gallardo (N73 million), Rolls Royce (N145 million), Polaris Slingshot (N8.7 million), Porsche Panamera (N29 million), Range Rover (N55 million),

Mercedes G-Wagon guda uku (N70 million ko wanne), Bentley Continental (N90 million), Chevrolet Corvette (N44 million), Ferrari (N100 million), 2 Mercedes E Class (N19.2 million each), da kuma Rolls Royce Phantom (N163.3 million).

 

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading