Sunayen Jihohin Arewa Maso Yamma Nijeriya

Kana Son Sanin Jerin Sunayen Jihohin Arewa Maso Yamma Nijeriya?

Nigeria na da yankuna shida (6), ne a rubuce, waɗan nan yankuna sune, A yankin Arewaci, Akwai Arewa maso Gabas, Arewa maso yammaci, da Arewa ta Tsakiya. Yankin kudu kuwa Akwai kudu maso gabas, kudu maso yammaci da kudu maso kudu.

A cikin wadannan yankuna shida, babu yankin da ta kai yankin Arewa maso yammaci, yawan al’umma, inda a wannan lokaci zamu lissafo Sunayen jihohin yankin, da kuma mu zamu duba ko jihohi nawa ne a yankin Arewa maso yammaci Nigeria.

 

Jerin Sunayen Jihohin Arewa Maso Yamma Nijeriyain:

  • Jigawa
  • Kebbi
  • Katsina
  • Kaduna
  • Kano
  • Sokoto

1. Jihar Jigawa

Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi masu fama da talauci a Nigeria. Kuma jihar an kirkiro ta ne daga jikin jihar Kano, a shekarar alif 1991. Yawancin al’ummar jihar Jigawa hausawa ne, kuma jihar ta dogara ne sosai a harkar noma da kiyo

 

2. Jihar Kebbi

Jihar Kebbi, ita ma jihar na kan iyaka ne. Jihar na daya daga cikin jihohi masu nomawa kasar Nigeriya, dama Afrika abinci, musamman ma noman shinkafa.Jihar Kebbi, mafi yawan jama’ar jihar Musulmai ne da hausawa.

3. Jihar Kaduna

Jihar Kaduna na yankin Arewa maso yammacin Nigeria. Jihar ita ce cibiyar masana’antu da kasuwanci, jihar ta yi saurin bunkasuwar birane da bunkasar tattalin arziki. Amma wasu na alakan ta haka ne, saboda suna kusa da babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja.

 

4. Jihar Katsina

Jihar ɗaya daga cikin jihohi da suke yawan al’umma a Nigeria. Jihar Katsina na da tarin tarihi da al’adu daban-daban, tun a lokacin da. Noma yana daya daga cikin muhimmin bangare na na tattalin arzikin jihar Katsina, inda jihar ke kan gaba har yanzu wajen noman gero da dawa. Jihar kuma gida ne ga shahararren mawakin nan, wato Rara.

 

5. Jihar Kano

Jihar Kano ita ce jihar da ta fi ko wane jiha da yawan al’umma a yankin, kuma na biyu a Kasar gaba daya. Jihar Kano na da tarihin tarihi tun da dadewa, jihar Kano ta yi suna sosai a bangaren kasuwanci.

Jihar Kano na da babban kasuwa a yankin Arewacin Najeriya, wato Kasuwar Kurmi. Jihar Kano ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kasuwanci, kuma jihar Kano gida ne ga attajirin ɗan kasuwan nan, wato Aliko Dangote.

 

6. Jihar Sokoto

Jihar Sokoto, tana can ne a yankin Arewa maso yammacin Nigeria, inda take kan iyaka da ƙasar Nijar. Ana wa jihar Sokoto ne da Kujerar Halifanci’, dalilin yi ma jihar lakabi da wannan suna shi ne saboda jihar na tarihi da dimbin al’adun Musulunci. bayan haka jihar gida ne ga Sarkin Musulman Nijeriya.

Jihohin kabilar Yoruba

7. Jihar Zamfara

Jihar Zamfara ita ce jiha daje kan gaba a bangaren rashin tsaro da kwanciyar hankali a cikin shekaru uku da suka gabata, a Nigeria gaba daya.

Jihar na daya daga cikin jihohi da suka fi kowane arzikin ma’adanai masu daraja na cikin kasa.

Karanta: manyan jihohin arewa 

Jihohin Yan kabilar Igbo 

 

Jihohi nawa ne a yankin Arewa maso yammacin Nigeria?

Jerin Jihohin Arewa ta Yamma, Sune:

  • Jigawa
  • Kebbi
  • Katsina
  • Kaduna
  • Kano
  • Sokoto
  • Zamfara

 

Jihohin Arewa ta Tsakiya 

 

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading