Cikekken: Tarihin Annabi Yusuf

Tarihin ANNABI YUSUF 25

Wane ne Annabi Yusuf? A cewar Alqur’ani mai girma da kuma masana da dama irin su ‘Ibn Kathir’ inda ya bayyana cewa ‘ Annabi Yakubu yana da ’ya’ya goma sha biyu wanda kuma su ne manyan kakannin kabilan Isra’ilawa kuma mafi girma da daraja daga cikin su shi ne annabi Yusufu.

Yusuf annabin Allah ne kuma daya daga cikin manyan annabawa da suka bar tarihi anan duniya har zuwa ranar karshe. Annabi Yusuf wato ɗan ɗan Yakubu ɗan Ishaku kuma ɗan Ibrahim. Annabi Yusuf an yi ta ambatar sunayen sa a cikin Alqur’ani mai girma.

 

Bayanan Annabi Yusuf

Suna: YUSUF 

Wurin Haihuwarsa: Palestine (Canaan)

Wurin Rasuwarsa: Misra (Egypt)

Sunan Babban Sa: Annabi Yakub

Sunan Mahaifiya: Rahila (Rachel)

Sana'a: Da'awa da Annabci

Ya’yan Sa: ?

 

 

Farkon Tarihin Annabi Yusuf Daga Kur’ani

Kamar yadda yake a cikin Alkur’ani mai girma sura ta goma sha biyu (12). Surar Annabi Yusuf daya ce daga cikin surorin Makki na Alqur’ani mai girma wacce take da ayoyi 111 kuma tana cikin kashi na 12 da 13. Wannan sura kuma ita ce sura ta hamsin da uku da aka saukar wa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

 

Wannan sura ta yi bayani filla-filla game da bangarori daban-daban na rayuwar Annabi Yusuf, wadanda bisa ga aya ta uku a cikin surar, ana kiranta da “Ahsan al-Qasas” (mafi kyawun labari). Mafi kyawun labari domin yana cimma manufar kissoshin Alqur’ani, watau koyan darasi a matsayi mafi girma.

Labarin Annabi Yusuf a cikin wannan sura ya fara ne da mafarkinsa, inda Kashi na biyu na labarin shine kishi da hassadar da yan uwansa suka jefa Annabi Yusuf cikin rijiya. An ceto Annabi Yusuf daga rijiya aka sayar da shi a kasar Masar, bayan sayar da shi a kasar Masar matar sarkin Masar na wancan lokacin wato Zuleykha ta kamu da son Annabi Yusuf.

 

Inda ta dalilin son da matar sarkin Masar wato Zuleykha, take wa Annabi Yusuf ne ya zamo dalilin da yasa Sarkin Masar ya rufe Annabi Yusuf a a gidan kurkuku, sakamakon sharrin da matar ta kulla masa, na cewa Annabi Yusuf ya nemi aikata lalata da ita, inda ita kuwa take kokarin guduwa domin guje wa haka, Inda daga karshe Sarkin Masar ya amince da da maganar matar sa Zuleykha.

Kuma Sarkin Masar ɗin ya karbi maganar matar sa Zuleykha na cewa kada kashe shi, kawai a tura shi gidan kurkuku. Bayan kasancewa a gidan kurkuku, a shekarar sa na farko a gidan kurkuku ne, Annabi Yusuf fassara mafarkin mutane biyu da suka dakin kurkuku guda, bayan fassarar mafarkin ne mutane suka yi ta mamaki har yaje kunnen sarkin Masar. Annabi Yusuf yazo ya fassarar mafarkin Sarkin Masar, daga nan komai ya fara yi wa Yusuf haske inda daga karshe Annabi Yusuf ya karbi mulki a Masar.

 

 

Cigaban Tarihin Annabi Yusuf bayan Zargin Bilyamin Da Yin Sata

 

Ci Gaban Tarihin Daga Sheikh MANSUR SOKOTO MNI:

Bayan da ‘yan uwan Annabi Yusuf suka gama zargin Bilyamin bisa tabbacin su da cewa shine ya yi satar, sai kuma suka dawo tunanin yadda za su fuskanci mahaifinsu idan sun koma gida.

Don haka suka hada bakinsu a kan su nemi minista ya musanya shi da dayansu. Annabi Yusuf alaihis salam ya ce, ina! Ai sam wannan ba adalci ba ne, mu saki wanda muka kama da kayanmu mu dauki wani a madadinsa? Suka ce, Allah ya taimake ka, babbar matsalar ita ce mahaifinsa tsoho ne sosai kuma yana cike da damuwa a kan rabuwa da shi.

 

Suka ci gaba da cewa “Don haka mu dai muna neman alfarma. (Suna fadin wannan maganar ne a cikin tsananin nuna damuwa kamar za su yi kuka). Annabi Yusuf alaihis salam ya ce masu, babu wani kukan da zaku yi min wanda zai sa in yi zalunci.

Da suka hakikance lallai ba zasu iya shawo kansa ba sai suka yi hakuri suka kebance suna tattaunawa don samun mafita. Babbansu shi ne Róbíl, ya yi jawabi yana tuna masu irin kakkarfan alkawarin da suka dauko a wurin mahaifinsu kan wannan yaro. Ya ce, kuma ku tuna irin sakacin da kuka yi game da Yusuf tun can da farko. Ya ce, ni kam ba zan koma gida ba saboda ina jin kunyar sa, sai fa idan shi ne da kansa ya nemi da koma.

Karanta: sunayen Maza Da Ma’anarsu a musulunci 

 

Ya ci gaba da cewa; ku tafi wurin babanku ku sanar da shi halin da ake ciki. Ku fada masa cewa, dansa ne ya yi sata, kuma mu, bamu san abinda ake ciki ba sai da aka kama shi. Amma don samun tabbaci ka nemi ayarin da muka yi tafiya tare da su ko ka aika a tambayo mutanen kauyen da aka tare mu a cikin sa. Kuma wallahi, mu masu gaskiya ne.

Yan uwan Yusuf su tara (9) ne suka iso gida da jiki a sanyaye, suka rattaba mahaifinsu wannan bayani kamar yadda Róbíl ya tsara masu. Annabi Ya’kub ya buga tasalima ya ce, na san za ayi haka. Kawai dai rayuwarku ce ta kawata maku wani abu, amma zan mayar da lamarina ga Allah in yi hakuri, watakila Allah zai dawo min da su gaba daya.

 

Sannan ya juya ya rabu da su yana juyayin wannan halin bakin ciki da ya shiga yana fadin “Ya kaicona a kan rashin Yusuf!” Saboda yawan kuka har sai da ganinsa ya samu tangarda. Su kuma ba su gushe ba wannan alhinin nasa yana ba su haushi har suna cewa, “Mun rantse da Allah idan ba ka daina wannan begen da kake yi da kuka a kan Yusuf ba zai iya halaka ka.

Babu abinda yake ce masu sai dai ku je ku yi ta sha’aninku, ni a wurin Allah nike kai kukana da neman yaye damuwata, kuma hakika na san abinda ba ku sani ba daga wurin Allah. Yana nufin cewa, ya san Yusuf yana nan da ransa kuma la-budda watarana za su hadu. Ko kuma yana nufin cewa, kuranye bakin ciki ga wanda yake kiran Allah yana kusa.

 

Jim kadan bayan dawowarsu, sai mahaifin nasu ya sake neman su da su hanzarta su sake komawa Masar, a wannan karon ba da zimmar su sayo abinci kawai ba, a’a har da zancen bin sawu ko da Allah, a cikin rahamarsa zai sa su yi gamon katar da dan uwansu Yusuf, sannan su kokarta su samu belin kanensu Bilyamin, in ya so sai su dawo tare har da Róbíl wanda ya makale a can ya ce ba zai dawo ba sai da umurnin babansa.

 

Annabi Ya’kub ya yi sallama da su ya yi masu addu’asannan ya ce, kada ku taba yanke kauna ga rahamar Allah, domin babu mai yin haka sai kafirai. Da suka isa Masar kai tsaye sai suka tasar ma ofishin minista suka surmuya suka gaida shi kamar yadda suka saba, sannan suka koka masa irin halin da suke ciki na karancin abin lalura tun daga kansu har iyalansu da iyayensu da suka baro a can gida.

Suka kara da cewa duk da ‘yan kudin da muka zo da su ba su taka kara suka karya ba. Don haka, muna rokon mai alfarma minista ya ci gaba da kyautata mana don Allah, kamar yadda ya saba, kuma ya kara mana da sadaka domin Allah yana saka ma masu yin sadaka da alheri.

 

Budar bakinsa sai ya ce masu, kun tuna ranar da kuka fita da Yusuf da hantsi bayan kun nemi izinin babansa da kakkarfan alkawarin cewa zaku kiyaye shi, kuka bi ta wajen bishiyar kuka, kuka tsaya kuna shawara, wane ya ce kaza wane ya ce kaza, kai wane har ka sa hannu ka dangware shi a goshi? Tsarki ya tabbatar ma Allah! A nan ne fa duk iyakar gudunsu ya kare. Suka ce, a’aha! Wai ko kai din ne Yusuf?

 

Ya ce, ni ne Yusuf, ga kuma dan uwana Bilyamin nan a cikin ofis yana tare da ni. Lallai kam Allah ya yi mana baiwa. Ku sani duk wanda ya ji tsoron Allah kuma ya yi hakuri, to, Allah ba ya tozarta ladar masu kyautatawa. Suka ce, tab! Lallai hakika, Allah ya zabe ka a kan mu, kuma hakika mun tafka babban laifi.

Annabi Yusuf ya ce musu, ku kwantar da hankalinku, babu wata damuwa; Allah zai gafarta maku don shi ne mafi jinkan masu jinkai. Sannan ya zo da wata rigarsa ya ce da su, ku je ku dan sarara sannan ku koma gida da wannan rigar sai ku jefa wa mahaifina ita, ganinsa zai dawo masa ras, kuma ku kwaso duk iyalanku gaba daya ku dawo da su nan wurina.

 

Tun fitar su daga cikin Masar zuciyar Annabi Ya’kub ta shako kanshin rigar dansa har ya kasa hakuri ya ce da sauran mutanen gidan, hakika ina jin kanshin Yusuf ba don na san zaku zolaye ni ba. Suka ce, kai kam wallahi har yanzu kana nan nutse a cikin tekun dimuwa.

To, da shi wanda zai yi albishir din dauke da rigar Yusuf ya iso sai kawai ya jefa ma Annabi Ya’kub ita kamar yadda Yusuf ya yi umurni, sai ya zabura idonsa ya bude yana cewa, ashe ban gaya maku ina da wani ilimi daga wurin Allah ba wanda ba ku da shi?

 

Suka sunkuyar da kansu saboda jin kunya suna cewa, ya kai babanmu, yanzu dai ka rokar mana gafarar Allah, tabbas mun tafka laifi. Annabi Ya’kub ya ce kada ku damu, zan roka maku gafarar Ubangijina domin shi mai gafara ne mai jinkai. Iyalan gidan Ya’kub gaba daya suka shirya tafiya zuwa Masar, suka kwashe komai da komai suka tafi da ‘ya’ya da jikoki da ‘yan dabbobin da suke kiyo. Suka yi bankwana da makwauta suna nufin hanyar babban birnin Masar.

Kafin su isa Annabi Yusuf alaihis salam ya shirya tsaf domin tarbon su. Ya sa aka fita kan hanyarsu ta shigowa gari aka kafa tanti-tanti aka kawata su, aka shimfida tabarmin alfarma irin na sarauta da kasaita, mutane masu dinbin yawa suka fito domin taya Yusuf tarbarsu, aka zo da abinci iri iri kamar yadda ake yi idan an zo tarbar Sarki.

 

Da suka iso Annabi Yusuf Alaihissalam ya taso ya rungume iyayensa yana zubar da hawayen farin ciki irin na wanda yake cike da shauki bayan rabuwa ta lokaci mai nisa. Ya ce masu ku shigo Misra kuna cikin aminci da yardar Allah. Sannan ya daga iyayensa bisa karagar sarauta irin wadda ministoci suke hawa. A nan ne fa mahaifinsa Annabi Ya’kub da mahaifiyarsa Ráhila tare da sauran ‘yan uwansa goma sha daya (11) duk suka surmuya suna sujuda ta girmamawa a gare shi (ba a haramta wannan ba a wancan lokaci).

Jerin sunayen maza a Islam 

Annabi Yusuf ya ce, ya kai babana! Wannan ita ce fassarar mafarkina. Ga shi nan Allah ya tabbatar da shi. Kuma hakika Allah ya kyautata min da ya fitar da ni daga kurkuku, kuma ya zo min da ku daga kauye kuka dawo birni, bayan can a baya Shaidan ya shiga tsakani na da ‘yan uwana. Hakika, Ubangijina mai tausayawa ne ga abinda ya so, kuma shi ne mai cikakken sani da gwaninta.

Sannan Annabi Yusuf ya shiga munajati da Ubangijinsa yana gode ma Allah bisa duk ni’imomin da ya yi masa har zuwa dora shi a kan mulki da ya yi da sanar da shi fassarar mafarki. Sannan ya roki Allah cikawa da imani da mutuwa a tafarkin Musulunci, a ranar alkiyama kuma Allah ya hada shi da mutanen kirki.

 

Jerin sunayen mata a musulunci 

Darussan Dake Tattare DA Tarihin Annabi Yusuf:

  • Tarihin Annabi Yusuf alaihis salam na daga cikin mu’ujizojin Manzon Allah Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam saboda labarta wannan kyakkyawan labari ga wanda bai taba karanta littafi ko daya ba yana nuna Annabtarsa.
  • Tarihin Annabi Yusuf alaihis salam ya fara da mafarki ya kare da fassararsa. Ya fara da rabuwar masoya ya kare da haduwarsu. Ya ba da labarin Yusuf daga kuruciyarsa zuwa girmansa. Ya fayyace duk irin wahalhalun da ya sha da jarrabawoyin da ya gamu da su amma da ya yi hakuri sai Allah ya daukaka shi. Haka ne Allah yake saka ma masu hakuri. Don haka babban darasin wannan kissa shi ne muhimmancin hakuri.
  • A cikin kissar Annabi Yusuf an boye abubuwa da dama Allah ya bayyana su. An batar da Yusuf an ce Kura ta cinye shi, daga karshe Allah ya tona asirin. An zarge shi da neman matar maigidansa daga bisani wadda ta yi zargin da kanta ta wanke shi. An tuhumci Binyamin da sata amma gaskiya ta yi halinta. Mu iya sanin cewa, duk abinda aka boye shi saboda munakisa da cin zalun tabbas watarana sai Allah ya bayyana shi.
  • Kissar Annabi Yusuf ta nuna mana yadda rayuwa take canji akai akai daga wani yanayi zuwa wani. Kana talaka ko komo mawadaci, kana cikin kaskanci ka samu daukaka, bawa ya koma Sarki, kunci ya koma sauki, watarana fatara watarana arziki, watarana bakin ciki watarana murna, ana cikin fari a samu damina, kana boyon hali ko kana boye labari watarana da kanka za ka fito da shi. Saboda haka babu abinda yake tabbas a duniyar nan bai canjawa. Idan ka shiga halin damuwa ka koma ga Allah domin shi ne ya ce: “lallai a tare da tsanani akwai sauki” Suratus Sharhi 5-6

Sunayen mata da ma’anar su

 

  • Mafarki shi ne jigon kissar Annabi Yusuf. Riga kuma ita ce ta taka muhimmiyar rawa a cikin tarihin. Da ita aka yi alamar Kura ta cinye shi, da ita aka gano Zulaikha ta yi masa kazafi, kuma da ita ne bushara ta zo ga mahaifinsa cewa yana nan a raye.
  •  Fassarar mafarki ilimi ne mai daraja na wasu kebantattu daga cikin Annabawa da wasu kebantattu daga cikin malamai. Fassarar mafarki ya zama ilimi mai zaman kansa a duniyar Musulmi tun daga zamanin tabi’ai har zuwa yau. Ba a yin karyar sa, kuma ba a karyar iya fassara shi. Idan an yi ana gamuwa da matsala.
  • Ga alamu ‘yan uwan Annabi Yusuf sun fara da-na-sanin abinda suka yi ne bayan da suka ga sun rasa Binyamin ba da zabinsu ba. Suka rasa yadda za su tunkari mahaifinsu idan sun koma gida. A nan ne Róbíl ya ce: “ku tuna irin sakacin da kuka yi game da Yusuf tun can da farko”. Da yawa mai laifi ba zai yi saurin nadama a kan laifinsa ba sai can daga baya in wani dalili ya taso.
  • Idan mutum ya saba da yin karya ko ya fadi gaskiya ba lallai ne a gaskata shi ba. Lokacin da aka raba su da Binyamin duk abinda suka fada wa mahaifinsu gaskiya ne amma bai gaskata su ba duba da inda aka fito.
  • Bacewar da ta fi mutuwarsa zafi. Babu shakka da mutuwa ce Annabi Yusuf ya yi mahaifinsa ba zai shiga wannan tsananin damuwar da har zai rasa ganin idonsa ba saboda kuka.
  • Irin tsananin halin damuwa da Annabi Ya’kub ya shiga a kan rabuwar sa da Yusuf ta nuna cewa, yana cikin manyan ni’imomin Allah zama kusa da masoya. Wata ni’imar ba a sanin ta sai an rasa ta.
  • Soyayyar iyaye ga ‘ya’ya tana gaba da wadda ‘ya’ya suke yi ga iyaye. Idan ka kwatanta cewa, Annabi Ya’kub ne ya samu labarin Yusuf zaka ce girman shaukin da yake da shi ba zai bari ya yi jinkiri wajen isa zuwa wurin Yusuf ba.
  •  Wannan kissar ta karantar da mu girman sha’anin mulki da kasaitarsa. A maimakon Annabi Yusuf ya koma gida bayan ya gane ‘yan uwansa, su dai mahaifan nasa ne suka yi hijira zuwa inda Allah ya ba shi mulki. Mu kiyayi masu mulki, duk wanda ya yi jayayya da su a sha’anin mulkinsu ba zasu dauke shi da sauki ba.
  •  Komai girmanka dole ne ka girmama iyayenka. Annabi Ya’kub da iyalansa sujuda suka yi ma Yusuf saboda girman da Allah ya ba shi – da yake a lokacin ba a hana ba. Amma tare da haka sai da ya daukaka iyayensa ya dora su a kan karagarsa ta iko da kasaita don ya nuna ma duniya girman matsayinsu.
  • Girmama bako da tarbonsa tun daga wajen gari – idan ya cancanci haka – al’ada ce mai kyau da take nuna karimci da halin girma.
  • Hassada ga mai rabo taki ce. ‘Yan uwan Annabi Yusuf sun kore shi ne don gudun daukakar matsayinsa kawai a wurin mahaifinsu. Sai ga shi Allah ya daukaka shi a kan su, da kan mahaifinsu da ma kan sauran mutanen wannan lokaci.
  •  Dan girma a kullum aikinsa na girma ne. Dubi yadda Annabi Yusuf alaihis salam cikin kyaftawa da bismillah ya yafe ma ‘yan uwansa laifin da ya yi shekaru barkatai yana dandanar kudarsa, tun ba su roke shi ba.
  • Yana daga cikin kawaici, ka kauce ma ambaton abinda zai muzanta dan uwanka. A cikin ni’imomin Allah da ya ambata, Annabi Yusuf ya fadi fitar sa daga kurkuku amma bai fadi fitar sa daga rijiya ba, saboda in ya fadi haka ‘yan uwansa za su shiga tsarguwa.
  • Sifaita ‘yan uwan Yusuf da taurari a cikin mafarkinsa ya nuna cewa, Allah ya karbi tubansu daga laifin da suka yi tun kafin su dawo Masar su yi masa sujuda. Ga shi kuma dan uwansu ya yafe masu, mahaifinsu ma haka. Babu shakka Allah yana daukaka mai laifi bayan an wanke shi daga laifinsa ta hanyar tuba da nadama da komawa ga Allah. Wasu malamai ma suna ganin cewa, Allah ya ba su Annabta a bayan haka. Sani na wurin Allah.

 

  • Gamji babbar inuwa. Idan Allah ya daukaka mutum daya a gida duk inuwarsa ta ishe su. Mu roki Allah ya ba mu ‘ya’ya da dangi masu albarka.

 

  • Ana son mumini ya zama mai godiya ga ni’imomin Allah. Kamar yadda Annabi Yusuf alaihis salam yake ta maimata ni’imar Allah da baiwarsa a kan sa tun daga sadda ya bar gida zuwa lokacin sake haduwarsa da ‘yan uwa da iyayensa.

 

  • Duk abinda ka samu a duniya kai dai nemi cikawa da imani. Wannan ita ce fatar Annabi Yusuf ta karshe kamar yadda muka gani a munajatin da ya yi da Ubangijinsa. kuma Allah ya hada shi da mutanen kirki.”

Marubuci: Sheikh Mansur Sokoto Mni

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button

Discover more from Arewa Voice

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading