Site icon Arewa Voice

Jerin sunayen Jihohin Arewa & Tarihin Arewa

Sunayen Jihohin Arewa Ta Tsakiya 

Arewa

Takaitaccen Tarihin arewacin Nigeria

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar alif 1897, ne Frederick Lugard ya ayyana aniyar sa na kare yankin Arewacin Najeriya, Kuma yankin Arewacin Najeriya ta kasance yanki ne mai cin gashin kanta a wancan lokacin. kuma haka ya samo asali ne biyo bayan yerjejeniyar Berlin da ya gudana a shekarar 1885, wadda hakan ya bai wa yankin Arewacin Najeriya zama a karkashin mulkin Birtaniya.

Kuma gwamna Frederick Lord Lugard ne ke kula da yankin Arewa ta hanyar amfani da sarakunan yankin, irin su sarakunan gargajiya, wadda ake kira “indirect rule” da turanci, wannan shi ne hanyar da turawar mulkin mallaka suka bi sa’annan suka samu nasarar mallakar yankin Arewa a wancan lokaci. Sunyi amfani da sarakuna masu karfi na wancan lokaci irin su Khalifancin Sakkwato da wasu sassan daular Bornu wadda aka fi sani da bornu empire.

Jihohin da suka fi kwanciyar hankali a Nigeria 

 

Jerin Jihohin Arewa:

Yankin Arewacin Najeriya na da jihohi goma sha tara (19), kuma wadannan jihohin sune kamar haka:

 

1. Jihar Adamawa

Jihar Adamawa ita ce jiha ta farko na Jerin sunayen Jihohin Arewa & Tarihin Arewa, jihar na yankin arewa maso gabashin Najeriya, an kirkiri jihar Adamawa ne a shekarar alif 1991. inda aka cire Jihar Taraba daga cikin Jihar Gongola a shekarar 1991, sai aka mayar wa Jihar Gongola suna zuwa jihar Adamawa.

Sunan babbar birnin jihar shi ne Yola. Kuma jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowane jiha yawan kabilu a Nigeria.

 

2. Jihar Bauchi

Jihar Bauchi wacce babban sunan birninta Bauchi, ita ma tana yankin a arewa maso gabashin Najeriya. Kuma an kafa jihar ne a ranar 3 ga Fabrairun a shekarar alif 1976 daga cikin tsohuwar jihar Arewa maso Gabas.

Kuma tun asali a da jihar Bauchi dama tana cikin jihar Gombe na yanzu, wadda ta zama jiha mai zaman kanta a shekarar alif 1996.

 

3. Jihar Benue

Jihar Benue na yankin Arewa maso Tsakiyar Nigeria. An kirkiro jihar Benue ne a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar alif 1976 daga cikin jihar Plateau a lokacin. Kuma galibin al’ummar jihar Benue yan kabilar Tiv,Idoma da Igede ne.

Babban birnin jihar Benue shi Makurdi, inda jihar ta hada iyaka da jihar Plateau, jihar Nassarawa, jihar Ebonyi da sauran su.

 

 4. Jihar Borno

An kirkiri jihar Borno ne a ranar 3 ga Fabrairun na shekarar alif 1976 daga tsohon yankin Arewa maso Gabas. Kuma galibin al’ummar jihar Borno yan kabilar Kanuri ne. Kuma sunan babbar birnin jihar ita ce Maiduguri.

Kuma an kirkiri jihar Yobe ne daga cikin jihar Borno a shekarar alif 1991. Jihar Borno ta hada iyaka da jihohi irinsu jihar Adamawa, jihar Gombe, jihar Yobe da ƙasar Kamaru.

5. Jihar Gombe

Gombe na yankin arewa maso gabashin Najeriya. An kirkiri jihar Gombe ne daga cikin jihar Bauchi a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar alif 1996, a wancan lokaci, kuma sunan babbar birnin jihar shi ne Gombe.

 

6. Jigawa State

Jihar Jigawa na yankin arewa maso yammacin Nigeria, kuma an kirkiro jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agusta cikin shekarar alif 1991, daga jikin jihar Kano. Sunan babbar birnin jihar shi ne Gusau, kuma galibin al’ummar jihar hausawa ne.

Sanatoci mafi dadewa a kan mulki 

 7. Jihar Kaduna State

Jihar Kaduna tana a Arewa maso yammacin Najeriya. An kirkiro ta ne a ranar 27 ga Mayun 1967 daga rabar yankin Arewa ta tsakiya daga shekarar alif 1967 zuwa 1976. Babban birnin jihar Kaduna shi ne birnin Kaduna.

Jihar Kaduna ta hada iyaka da jihohi irinsu jihar Kano, jihar Katsina, jihar Sokoto, jihar Plateau, jihar Neja da babbar birnin tarayyar Nigeria Abuja.

Jerin manyan Jihohin Arewacin Najeriya

 

 8. Jihar Kano

An kirkiro jihar Kano ne a ranar 27 ga Mayun shekarar alif 1967 daga tsohon yankin Arewa na wancan lokacin. Jihar Kano tanana yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya kuma jihar ita ce jiha mafi bunƙasa a yankin Arewacin Nigeria inda yawanci al’ummar jihar Kano Hausawa ne.

Manyan hotel hotel da ke jihar Kano

Jihar Kano ita ce mafi yawan jama’a a yankin Arewacin Najeriya inda Jihar ta hada iyaka da jihar Katsina daga arewa maso yamma, jihar Jigawa a arewa maso gabas, jihar Bauchi a kudu maso gabas da kuma jihar Kaduna a kudu maso yamma.

 

 9. Jihar Katsina

An kafa jihar Katsina ne a ranar 23 ga watan Satumban shekarar alif 1987. Inda aka kirkiro jihar daga cikin jihar Kaduna. Kuma sunan babbar birninta shi ne Katsina.

Jihar Katsina tayi iyaka da jihohi irinsu jihar Kano, jihar Zamfara, jihar Kaduna, jihar Jigawa da kasar Nijar.

 

10. Jihar Niger

Jihar Niger dake yankin Arewa maso Tsakiyar Nigeria, an kafa jihar Neja ne a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar alif 1976, daga tsohon jihar Arewa maso Yammaci a wancan lokaci. Babban birnin jihar Neja shine Minna.

 

11. Jihar Kebbi

An kafa jihar Kebbi ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar alif 1991. Inda aka kirkiro jihar daga cikin jihar Sokoto. Jihar Kebbi na yankin arewa maso yammacin Najeriya kuma babban birnin jihar shi ne shine Birnin Kebbi.

Jerin Yan Siyasa 7 Da Suka Mallaki Jirgi (Private Jet) A Nigeria

 

12. Kwara State

An kirkiro jihar Kwara ne a ranar 27 ga watan mayu cikin shekarar alif 1967, daga yankin Arewa a wancan lokacin. Jihar Kwara na yankin arewa maso tsakiyar Nigeria. Kuma sunan babbar birnin jihar shi ne Illorin.

Duk da jihar kwara na yankin Arewacin Najeriya, amma jihar gida ne ga yan kabilar yarabawa.

 

13. Nasarawa State

Jihar Nasarawa dake yankin Arewa maso Tsakiyar Nigeria, wanda sunan babbar birnin jihar shi ne Lafiya. An kafa jihar Nasarawa ne a ranar 1 ga watan Oktoba a shekarar alif 1996. Inda aka kirkiro jihar daga cikin jihar Plateau.

Jihar Nasarawa ta hada iyaka da jihar Kaduna ta arewa, jihar Kogi da jihar Benue ta bangaren kudu, daga gabashi kuma akwai jihohin Taraba da Filato sa’annan kuma sai babbar birnin tarayya Abuja daga yammaci.

 

14. Jihar Plateau

Jihar Plateau dake yankin Arewa maso Tsakiyar Nigeria, wanda sunan babbar birnin jihar shi ne Jos. An kafa jihar Plateau ne a ranar q ga watan Oktoban shekarar alif 1996. Jihar Plateau ta hada iyaka ne da Jihohi irin su jihar Bauchi, jihar taraba, jihar Kaduna, jihar Gombe, jihar Benue da jihar Nassarawa.

 

 15. Jihar Kogi

Jihar Kwara da ke yankin Arewa maso Tsakiyar Nigeria, An kirkiro jihar Kogi ne daga cikin sassan jihohin Kwara da kuma Benue a wancan lokaci. Jihar kwara ta hada iyaka ne da jihohi irinsu jihar Niger, jihar kogi, jihar Ekiti, jihar Oyo da babbar birnin tarayya Abuja.

 

 16. Jahar Sokoto

An kafa jihar Sokoto ne a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar alif 1976, daga yankin Arewa maso Yammaci na wancan lokacin. kuma jihar Sokoto ta kasance babban birnin tsohuwar jihar Arewa maso yammaci na wancan lokaci. Babban birnin jihar Sokoto shine Sokoto, kuma jihar ta kan iyakarta kasar Nigeria da Nijar.

Jihohin Arewa ta Tsakiya

 17. Taraba State

Jihar Taraba da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wanda aka kirkiro ta daga tsohuwar jihar a ranar 27 ga watan Agustan shekarar alif 1991. Daga tsohuwar jihar Gongola a wancan lokaci, Gongola da ta kunshi jihohin Adamawa da Taraba.

 

 18. Jihar Yobe

Jihar Yobe na yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma an kirkiro jihar Yobe ne daga jikin jihar Borno a ranar 27 ga watan Agustan shekarar alif 1991, Kuma sunan babbar birnin jihar shi ne Damaturu. Jihar ta hada iyaka ne da Jihohin Gombe, jihar Bauchi, jihar Jigawa da jihar Borno.

 

19. Jahar Zamfara

An kafa jihar Zamfara ne daga tsohuwar jihar Sokoto a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar alif 1996, babban birninsa jihar shi ne Gusau.

Jihar Zamfara na kan iyakar Nijeriya da jamhuriyyar Nijar. Kuma ita ce jiha ta karshe a rubutun mu na Jerin sunayen Jihohin Arewa & Tarihin Arewa.

 

 

Asalin Jihohin yan kabilar Yoruba

 

Exit mobile version