Cikekken jerin sunayen arewa ta tsakiya shine:
-
Jihar Benue
-
Jihar Niger
-
Jihar Kwara
-
Jihar Nasarawa
-
Jihar Plateau
-
Jihar Kogi
1. Jihar Benue
Babban birnin Benue State shi ne Makurdi kuma jihar tayi iyaka da jihohi irinsu; Plateau State, Nassarawa state, Ebonyi state etc. Benue State tana nan a yankin Arewa ta Tsakiyar Nigeria. galibin mutanen da suke jihar Benue yawanci yan kabilar Tiv, Idoma da Igede da sauran su ne.
2. Jihar Niger
An kirkiro jihar Niger ne a ranar uku (3) ga watan Fabrairun shekarar 1976, daga tsohuwar jihar Arewa maso Yamma na wancan lokaci. Kuma jihar Niger ta haɗa iyaka da babbar birnin tarayyar Nijeriya Abuja.
3. Jihar Kwara
Sunan babbar birnin jihar Kwara ita ce Illorin, inda jihar ta haɗa iyaka da jihohi da ga yankin kudu, musamman ma jihohin yarabawa. An kafa jihar Kwara ne a ranar ashirin da bakwai ga watan Mayun shekarar alif 1967.
4. Nasarawa State
Jihar Nassarawa ta haɗa iyaka da jihohi irinsu Plateau State, Benue State, kuma ta haɗa iyaka da babbar birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.
An kafa jihar Nasarawa ne a shekarar alif 1996 daga jikin jihar plateau State.
6. Jihar Plateau
An kirkiro jihar Plateau ne a watan Oktoban shekarar alif (1996). Jihar na yankin Arewa ta Tsakiyar Nigeria ne, kuma kuma sunan babbar birnin jihar shi ne, Jos, inda jihar ta haɗa iyaka da jihohin! Kaduna, Gombe da Nassarawa.
Jerin sunayen manyan jihohin arewa
7. Jihar Kogi
Mafi yawan jama’ar jihar kogi yan kabilar yarabawa ne. An kafa jihar Kogi ne daga jikin Benue. Inda jihar kogi ta haɗa iyaka da jihohi da suka haɗa da kwara state da wasu jihohin yarabawa da ke yankin kudu. Kuma jihar na kogi, na daya daga cikin jihohin da suka fi yawan kwanciyar hankali a Nigeria.
Jihohi arewa ta tsakiyar guda nawa ne?
jerin sunayen arewa ta tsakiyar Nigeria sune:
- Benue State
- Niger State
- Kwara State
- Nasarawa State
- Plateau State
- Kogi State