Site icon Arewa Voice

Jerin Sunayen Manyan Jihohin Arewa – Nigeria

Full List of All Nigerian Languages

 

Tarayyar Nigeria ita ce kasa mafi yawan jama’a a yankin Afirka, na farko da tafi kowace kasa yawan bakaken fata a duniya, kuma ita kasa ta bakwai mafi yawan al’umma a fadin duniya. Kasar Najeriya tana da yawan al’umma da ta kai sama da mutane miliyan 200.

Nigeriata kasa ce dake da kabilu, harsuna da al’adu da dama kuma daban-daban, kuma tana addinai da suka rarrabu zuwa kashi uku, wato addinin Kiristanci, Musulunci da kuma addinin gargajiya.

A wannan rubutun zamu duba jerin sunayen manyan jihohin yankin Arewacin Najeriya, bisa yawan jama’a.

 

Manyan Jihohin Najeriya:

 

An kirkiri jihar Kano ne a ranar 27 ga watan Mayun shekarar alif 1967. Jihar Kano ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya kuma jiha mafi yawan bakaken fata a duniya, kamar yadda hukumar kidayar yawan jama’a a shekarar 2019 suka gudanar. Kuma jihar Kano ita ce jiha mafi arziki a yankin Arewacin Najeriya kuma ita ce jiha ta shida (6) a Najeriya.

Jihar Kano tana a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda jihar ta hada iyaka da jihohi irinsu: jihar Katsina ta yankin Arewa maso gabashi, jihar Jigawa ta yankin kudu maso yammaci, jihar Bauchi ta yankin kudu maso gabashi da jihar Kaduna ta yankin kudu maso yammacin jihar.

 

Jihar Katsina dake yankin arewa maso yammacin Nigeria, ita ce jiha na uku wajen yawan al’umma a yankin arewaci, kuma na hudu a fadin Nigeria. An kafa jihar Katsina ne a ranar 23 ga watan Satumba a shekarar alif 1987.

Inda jihar tayi iyaka da jihohin kano, jihar Kaduna, jihar Zamfara jihar Jigawa da kuma kasar Niger.

 

An kirkiri jihar Kaduna ne a ranar 27 ga watan Mayun shekarar alif 1967. Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar Nijeriya, ita ce jiha ta biyu (2) da ta fi yawan al’umma a arewa, kuma na uku (3) mafi yawan al’umma a Nigeria. Kuma jihar Kaduna ita ce jiha mafi bunƙasa a yankin Arewacin Nigeria.

Jihar Kaduna tana da kabilu da harsuna daban daban, amma kuma Hausawa ne suka fi yawa a jihar. Kaduna tana da gidajen gwamnati da dama ciki akwai, barikin sojoji da ma Sansanonin su, akwai manyan makarantu da suka da Kwalejin Tsaro ta Najeriya, Kwalejin Fasahar Jiragen Sama da babbar Jami’ar Ilimi ta Ahmadu Bello University.

Jihar Bauchi na daya daga cikin manyan jihohin da suka fi yawan al’umma a yankin arewa da ma Nigeria. An kirkiri jihar Bauchi ne a ranar 3 ga watan Fabrairu shekarar alif 1976, daga cikin tsohon yankin Arewa-maso- gabashi. An kirkiri jihar Bauchi ne daga jikin jihar Gombe na yanzu.

Jihar Bauchi ita ce jiha na biyar da tafi kowace jiha yawan mutane a Najeriya, kuma yawancin mutanen jihar Bauchi hausawa ne, inda jihar ta hada iyaka da jihohi irinsu: jihar Plateau, jihar Kano, jihar Yobe, jihar Kaduna da jihar Jigawa. Kuma mafi yawan ayyukan dake kawo wa jihar kuɗin shiga ita harkar noma da kiwo.

Jihohin yan kabilar Igbo

Jihar Jigawa daya ne daga cikin manyan jihohin da suka fi yawan al’umma a arewacin Nigeria, kuma daya daga cikin jihohin da suka fi yawan manoma a Nigeria. Inda jihar ta hada iyaka da jihohi irinsu: jihar Yobe, jihar Kano da jihar Bauchi.

Jihar Jigawa ta kuma haɗa iyaka da ƙasar Nijar ta yankin Arewa maso gabashi. An kirkiri jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar alif 1991. Inda aka ciro ta daga cikin jihar Kano. Kuma babbar birnin jihar Jigawa ita ce Dutse.

 

Jihar Neja ita ce jiha na daya a bangaren fannin kasa da girman yanki. Jihar Niger na yankin arewa maso tsakiyar kasar Nigeria, kuma gida ne ga tsohon shugaban kasar Nijeriya wato, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Jihar Neja ta hada iyaka da jihohi irinsu, jihar Kaduna, jihar Zamfara, jihar kwara, jihar Kebbi da babbar birnin tarayyar Nigeria Abuja. Kuma jihar gida ne ga yan kabilar Gwari.

 

Jihar Benue dake yankin Arewa maso Tsakiya, na daya daga cikin jihohin da suka fi yawan al’umma a yankin Arewa maso tsakiyar Nigeria, inda al’ummar jihar takai sama da miliyan hudu.

Jihar Benue tana da kabilu da harsuna daban daban ciki akwai hausawa, Fulani da ma sauran wasu yarurruka. Kuma jihar ta hada iyaka da jihohi irinsu jihar Taraba, jihar Nassarawa, jihar Plateau, jihar kogi da jihar Ebonyi. Ta kuma haɗa iyaka da ƙasar Kamaru.

 

Jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, tana daya daga cikin manyan jihohin da ke yankin Arewa maso gabashi. An kafa jihar Borno ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a shekarar alif 1976. Kuma daga jikin jihar Borno ne aka ciro jihar Yobe.

Mafi yawan jama’ar jihar Borno yan kabilar Kanuri ne, kuma jihar gida ne ga babban kasuwar nan mai suna ‘Monday market’, babbar birnin jihar Borno shi ne Maiduguri.

Jihohin da suka fi yawan kabilu a Nigeria

 

Jihar Sokoto dake yankin arewa maso yammacin Nigeria, na daya daga cikin jerin jihohin Arewa dake cikin jihohin da suke da yawan jama’a, inda jihar ke ci gaba da samun yawaitar al’umma, duk da rashin aiki da da matasan jihar ke fama da ita.

 

Jihar Zamfara, jiha ce dake Arewa maso yammacin Nigeria, kuma sunan babban birnin jihar shi ne Gusau. An kirkiri jihar Zamfara ne daga jikin jihar Sokoto a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar alif 1996.

 

Kebbi state was created on 27 August 1991 out of Sokoto state. It is located in north-western Nigeria and its capital is Birnin Kebbi. Kebbi State shares borders with Sokoto State, Niger State, and Zamfara State.

 

 

 

Exit mobile version