Site icon Arewa Voice

Sanatoci (8) Mafi Dadewa A Kujerar Majalisar Najeriya

Sanatoci
Yan majalisar dokokin Nigeria

Kundin tsarin mulkin ƙasar Najeriya ta bada dama ga duk ɗan majalisa zai cigaba da mulki idan har jama’a suka ci gaba da zabar sa, kama daga sanata zuwa yan majalisar dattawa. 

 

Ga jerin mu, na sunayen sanatoci takwas (8) Mafi dadewa a majalisar Najeriya.

 

1. Bukar Ibrahim, , Borno,(25 years)

Sanata bukar Ibrahim shine na farko a jerin mu Sanatoci (8) Mafi Dadewa A Kujerar Majalisar Najeriya, shine sanata mafi dadewa a tarihin majalisar Nigeria, inda ya wakilta ya hada jihar Borno da jihar Yobe. Bayan aikin da ya yi a matsayin ma’aikacin faran hula a jihar Borno daga shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas, ya zama Kwamishina. Haka kuma a shekarar alif dubu daya da dari tara da casain da tara 1999 ya zama gwamnan jihar Borno.

 

2. David Mark, Benue (PDP, 1999-2019)

Sanata David ɗan shekara 71 a duniya, Sanata David Alechenu Bonaventure Mark, shi ke wakiltar al’ummar mazabar jihar Benue ta Kudu a majalisar dattawa. Kuma Ya kasance a majalisar dattawa ne, tun dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 a karkashin jam’iyyar PDP. Sanata David dai tsohon ministan sadarwa ne a gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Babangida kuma tsohon gwamna ne na jihar Neja a lokacin ana mulkin soja. Bayan haka kuma An sake zaban shi a shekarar 2003, 2007, 2011, da kuma shekarar 2015. Bayan haka a shekarar dubu biyu da bakwai 2007, ya kara zama shugaban majalisar dattawa kuma ya rike mukamin ne na tsawon shekaru takwas, wannan ya bashi damar kasancewa zama shugaban majalisar dattawan Najeriya mafi dadewa. A shekara ta 2016 wata kotu ta soke zaben sa, ya fuskanci sake tsayawa takara a lokacin kuma ya sake kashewa. Shine sanata mafi daraja a Nigeria yanzu haka, Kuma shine kadai a tarihin Nigeria Ya taba sayawa zaben sau shida kuma ya lashe zaben gaba-daya.

 

 

3. Ahmad Ibrahim Lawan, Yobe (APC, 1999-kwana)

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, mai shekaru hamsin da bakwai (57) kamar David Mark shi ma ya zo Majalisar Tarayya a shekarar 1999. Yayin da aka rantsar da David Mark a matsayin dan majalisar wakilai, Lawan shima ya na da nasa a majalisar wakilai. Lawan yana da Digiri a Remote Sensing, kuma a shekarar dubu biyu da goma sha biyar shi ne dan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin dan takarar shugaban majalisar Dattawa na yankin sa.

 

4. Ike Ekweremadu Enugu (PDP, 2003-date)

Sanata Ike Ekweremadu, an haifi shi a shekarar 1963 a jihar Enugu, kuma Lauya ne wanda daga baya ya koma ya zama ɗan siyasa, a shekarar dubu biyu da uku 2003 an fara rantsar da shi ne a matsayin dan majalisar dattawan Enugu ta Yamma. bayan ya jagoranci karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu. A shekarar 2015 watan Yuni Ekweremadu ya hada kai da Sanatocin APC a lokacin domin ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa Najeriya lokacin da aka kaddamar da majalisar dattawa ta takwas. Kuma a halin yanzu, shi ne shugaban majalisar da ya fi dadewa a majalisar, inda ya yi shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin sanata David Mark.

Gwamnoni da ke kan mulki suka gaza lashe kujerar sanata

 

5. Ali Ndume Borno (APC, 2003-date)

Sanata Ali Ndume na jihar Borno an haifi shi a shekarar 1959, a shekarar dubu biyu da bakwai 2007 ya zama shugaban marasa rinjaye yayin da yake cikin Wata jam’iyyar All Nigerian Peoples Party (ANPP). an fara rantsar Ali Ndume a matsayin wakilin Chibok/Damboa/Gwoza a shekarar dubu biyu da uku 2003. Inda ya wakilci mazabar tarayya har zuwa shekarar dubu biyu da goma sha daya 2011 inda ya ci gaba da wakiltar mazabar Benue ta yankin Kudu. A shekarar dubu biyu da bakwai ya zama shugaban marasa rinjaye kuma ya ci gaba da zama a cikin rusasshiyar jam’iyyar All Nigerian Peoples Party (ANPP), yankinsa na daya daga cikin manyan yankuna shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015 da ta fama matsalolin tashin hankali yan kungiyar Boko Haram.

 

6. James Manager, Delta (PDP, 2003-date)

Sanata James manager, sanata ne dake wakiltar jihar Delta ta kudu, James manager yana da shekaru hamsin da shida (56) a duniya (56), an rantsar da shi a matsayin Sanata a shekarar dubu biyu da uku 2003, inda yake wakiltar Delta ta Kudu, kuma tun a wancan lokacin yana Majalisar Dattawa, kuma yana shugabantar kwamitoci daban-daban. James manager dai a bangaren karatu, yana da digiri har sau biyu, digiri nasa na biyu ya yi ta ne a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a jihar Kaduna.

 

7. John Owan Enoh, Cross River (APC, 2003-date)

Sanata John Enoh, shi ne ke wakiltar jihar Cross River ta yankin tsakiya, An haifi John Enoh a shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da shida 1966. An rantsar da sanata John Owan Enoh ran tara ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015. Kuma shine ke shugabantar kwamitin Kudi na majalisar dattawa, shima ya na daya daga cikin manyan yan siyasa a Nijeriya, kuma mafi dadewa a tarihin majalisar Nigeria.

 

 

8. Philip Tanimu Aduda, FCT (PDP, 2003-date)

Sanata Philip Tanimu Aduda, shine Sanatan da ke wakiltar babban birnin kasar Najeriya wato Abuja, an haifi Philip Tanimu Aduda a cikin garin Abuja a karamar hukumar Karu, kuma yana da shekaru arba’in da bakwai a duniya (47). A shekarar dubu biyu da uku 2003 ne aka soma ransar da shi, har zuwa shekarar alif dubu biyu da goma sha daya 2011. Abokanan aikinsa suna masa lakabi da kalmar ‘mai gida’ dalilin saka masa wannan lakabi kuma shine; sabida majalisar karan kanta a yankinsa take.

 

 

Me shawarar ku akan jerin mu naSanatoci (8) Mafi Dadewa A Kujerar Majalisar Najeriya?

Exit mobile version