Mun muku Jerin Yan Siyasa 7 Da Suka Mallaki Jirgi (Private Jet) A Nigeria, karanta a kasa.
Ga jerin Yan Siyasa 7 Da Suka Mallaki Jirgi (Private Jet) A Nigeria
1. Rotimi Amaechi
Tsohon gwamnan jihar Ribas dake yankin kudu maso Gabas, a shekarar dubu biyu da goma sha biyu 2012 an ce tsohon gwamnan, ya sayi sabuwar jirgi mai suna Bombardier Global 5000 (N565RS) wanda a asirce ya saye ta.
An ba da rahoton cewa Ministan na Sufuri na yanzu ya sayi jirgin ne kan kuɗi dala miliyan 50 a lolokacin.
2. Bola Ahmed Tinubu
Fitaccen dan siyasar Najeriya wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shine na farko a jerin mu na Jerin Yan Siyasa 7 Da Suka Mallaki Jirgi (Private Jet) A Nigeria, tsohon gwamnan jihar Legas sau Zango biyu a jere. Wadda a yanzu haka shine jam’iyyar APC suka sayar a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC. Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas din na da jiragen sama masu zaman kansu har guda biyu. Jet mai zaman kansa na biyu da Bola Tinubu ya saya shine sabon Bombadier Global Express XRS wadda ya ci masa dala miliyan 50 (N10 biliyan) a kuɗin Nigeria.
3. Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu yana daya daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Abia ne, ba a bar shi a cikin ‘yan Najeriyar da suka mallaki jiragen sama masu zaman kansu. An ruwaito cewa yana da jiragen sama masu zaman kansu har guda biyar. Wanda ya kafa (SLOK Holdings) kuma mamallakin gidajen jaridu guda biyu ne wato Daily Sun da New Telegraph a cikin hangar sa na Gulfstream G650 wanda ya sayi jirgin sama da dala miliyan 72, daya daga cikin jiragen sama mafi tsada a Najeriya.
4. Ali Modu Sheriff
Ali madu Sherif shima wani fitaccen dan siyasar Najeriya ne. Kuma tsohon gwamnan jihar Borno ne. Shima ya mallaki jirgin sama mai zaman kansa ( Private Jet), inda ya mallaki jirage har guda hudu, gami da Gulfstream G650 da jirgin Dornier guda uku.
Gulfstream G650 shine sabon jirgin da ya sayi a baya bayannan. Kuma farashin jirgin na asali yana kai sama da dala miliyan sittin da biyar 65.
5. Godswill Akpabio
Shahararren ɗan siyasa ne, kuma tsohon gwamnan jihar Akwa-ibom ne, Godswill Akpabio ya kasance mai yawan kashe kudi ne a rayuwarsa, kuma ya sayan wata sabuwar mota kirar Bombardier Global 5000 mai lamba N224BH, kuma ya saye ta da sunan wai motar mallakar gwamnati ce. Amma duk da haka a lokacin yana ghamnan jihar Akwa-ibom ya yi ta musu aiki sosai.
6. Prince Ned Nwoko
Shi dai Ned Nwoko ɗan siyasa, ɗan kasuwa ne kuma ɗan gidan sarauta ne, shi yarimar masarautar Anioma ne. Bayan haka Prince Ned Nwoko attajirin mai kudi sosai, kuma shine wanda ya auri Wannan babbar yar fim din da tayi duna sosai dake yankin kudu wato Nollywood wato ( Regina Daniel ). Prince Ned Nwoko dai ya mallaki jirgin sama mai zaman kansa wato (Private Jet). Kuma yana amfani da shi ne wajen taimaka masa wajen harkokin kasuwancin sa.
Sanatoci Mafi dadewa a majalisar dokokin Nigeria
7. Jide Omokore
Jide Omokore shima wani babban fitaccen dan siyasa ne, dan asalin jihar Kogi, kuma shine ya mallaki kungiyar Albarkatun Makamashi Jide Omokore. a wannan lokacin kuma an gano wani jirgin sama wadda mallakarsa ne jirgi Mai zawan kansa zaman kansa (Private Jet). Sai dai daga baya an gano cewa yana cikin abokan tsohon ma’aikacin man fetur na Najeriya wadda ake zarginss da kata almundahana.
Jerin sunayen Yan Siyasa Da Suka Fi Kuɗi A Nigeria