Jihar Kano ita ce jiha mafi yawan jama’a, kuma daya daga cikin jihohi mafi bunƙasa a arewacin Nijeriya. Kuma daya daga cikin jiha da jama’a ke yawan ziyar ta domin gudanar da harkokin kasuwanci, hutawa da ma sauran su.
Domin mutanen da ke son ziyar tar jihar Kano, musamman ma zuwan su na farko a wannan labarin zamu duba jerin sunayen masaukar baki na hotel hotel mafi kyau dake cikin Jihar Kano.
Ga Jerin Sunayen Hotel Mafi Kyau dake Jihar Kano:
- Tahir Quest House Palace
- Bristol Palace Hotel
- Prince Hotel
- GK Guest Palace
- Mozida Suites
- BON Hotel Kano
- R&K Guest Palace
- Porto Golf Hotels
- Niimah Guest Palace Annex
- Babale Suites
Tahir Quest House Palace
Hotel ɗin tahir quest house palace, shi ne hotel mafi kyau da shahara yanzu haka a jihar Kanon Nigeria. Tahir quest house ta samu karɓuwa daga wurin jama’a, daga sassa daban daban a fadin Nigeria dama duniya.
Jama’a suna nuna jin dadin su yayin zama a hotel din Tahir Quest house palace, musamman ma masu zuwa jihar domin gudanar da kasuwanci su.
Bristol Palace Hotel
Bristol Palace Hotel, na daya daga cikin shahararrun masaukar baki ko hotel hotel da ke birnin jihar Kano. Kuma jama’a suna ci gaba da nuna jin dadin su, ta yadda aka sarrafa hotel din da kayakin zamani masu ban sha’awa.
Prince Hotel
Masaukar baki ta, Prince Hotel na daya daga cikin manyan hotel hotel da jama’a ke yawan zirga-zirga zuwa wurin domin hutawa, kwana da sauran su. Prince Hotel, an sarrafa hotel din ne, da kayakin zamani masu kayatarwa.
GK Guest Palace
Hotel ɗin, GK Guest Palace ita ma tana daya daga cikin shahararrun masaukar baki dake birnin jihar Kano, wannan hotel din an kayatar da shi da kayayyakin zamani daban daban. Kuma yana da inganci yadda ake bukata.
Mozida Suites
Masaukar baki ta, Mozida Suites, hotel ne da aka sarrafa ta da kayayyakin zamani da aka kawo daga ƙasashen waje masu ban sha’awa. Kuma yana daya daga cikin hotel hotel mafi kyau a jihar Kanon Nigeria.
BON Hotel Kano
Masaukar baki ta, Bon Hotel Kano, na daya daga cikin manya kuma shahararrun hotel hotel da ke jihar Kano. Baki daga sassa daban daban a Nigeria suna sauka a hotel din, BON Hotel Kano.
R&K Guest Palace
hotel din, R&K Guest Palace, masaukar baki ne da jama’a daga ƙasashe da garuruwa daban daban ke yawan zirga-zirga zuwa wurin domin sauka, kuma yana daya daga cikin hotel mafi kyau a jihar Kano.
Porto Golf Hotels
Porto Golf Hotels, daya ne daga cikin masaukar baki da mutane suke yawan sauka, musamman ma masu zuwa Kano don harkokin kasuwanci da sauran su.
Niimah Guest Palace Annex
Masaukar baki ta, Niimah Guest Palace Annex ɗaya ne daga cikin hotel hotel da ake yawan amfani da shi domin hutawa, kwana da dai sauransu. Kuma yana daya daga cikin masaukar baki da ake yawan ziyar ta.
Jihohin da suka fi kwanciyar hankali a Nigeria
Babale Suites
Hotel ɗin, Babale Suites na daya daga cikin masaukar baki da jama’a ke yawan ziyar ta daga sassa daban daban domin sauka, musamman masu ziyar ta jihar domin harkar kasuwanci.
Wannan shi ne jerin mu na sunayen masaukar baki ta hotel hotel 10 da ke jihar Kano, amma akwai wasu manyan Hotel Hotel da bamu samu cikakken bayanai akan su ba.
Jihohin da suka yawan kabilu a Nigeria
Ga wasu daga cikin manyan Hotel Hotel da bamu saka sunayen su ba sun hada da:
- Grand Central Hotel
- Green Place Hotel
- Daula Hotel
- Babale Suites
- The Prestige Villa Kano
- Milton Park Hotel & Resort