Wane ne Ahmad Ali Nuhu?
Ahmad, ɗa ne ga shahararren jarumin fina finan Kannywood ta Hausa, wato Ali Nuhu wanda mabiyansa suke masa da suna da “sarki Ali”. An haifi Ahmad Ali Nuhu a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2006.
Bayanan Ahmad Ali Nuhu
Asalin Suna: Ahmad
Ranar Haihuwa: 30/5/2006
Suna Baba: Ali Nuhu Mohammed
Sunan Mama: Maimuna Abdulkadir
Sana’a: Kwallon kafa, jarumin Fim
Shekaru: 18
Wurin Haihuwa: Kano
Fina Finan Ahmad Ali Nuhu
Ahmad Ali Nuhu, ya fito a fina finan da suka haɗa da: Carbin Kwai, Zuri’a, Kara da Kiyashi, Akan Idona, Shakka da Uba da ‘Da ga darajarsa, da ma sauran su.
Shekarun Ahmad Ali Nuhu
An haifi Ahmad Ali Nuhu ne, a shekarar dubu biyu da shida 2006, inda a shekarar bana (2024) Ahmad na da shekaru goma sha takwas (18) ne a duniya.
Kungiyar Kwallon kafan Ahmad Ali Nuhu?
Ahmad Ali Nuhu tun yana ɗan karami Mahaifinsa wato jarumi Ali Nuhu ya saka shi a makarantar koyon kwallon kafa, inda yanzu haka Ahmad yana kungiyar koyon kwallon kafa ta Manchester United da ke kasar Ingila.