Alamomin Shigar Ciki A Satin Farko
Siffofin Mace Mai Ciki
Menene Ɗaukar ciki?
Ɗaukar ciki ko samun juna biyu shine Idan mace ko dabba tana da ciki, tana da jariri ko jarirai masu tasowa a jikinta, ciki yana ɗaukar kimanin kwanaki 288.
Ciki yakan ɗauki kimanin makonni arba’in (40), ko kuma ma sama da watanni tara (9), kamar yadda aka auna daga lokacin haila na ƙarshe.
Mene Siffofinsa Mace Mai Ciki?
Mafi yawan alamun farko da ake gane cewa mace tana dauke da juna biyu, akwai alamomi da dama da ke siffanta mace mai dauke da ciki, cikin wadannan alamun sun haɗa da:
Yadda Ake Gane Alamomin Shigar Ciki A Satin Farko:
Ɓatawan Wata: idan kina cikin shekarun haihuwa, mako guda ko fiye da haka ya wuce ba tare da fara hailar da ake tsammani ba, zai iya kasancewa kina ɗauke da ciki.
Canjin yanayin nono: musamman k’amar yawan ciwon nono da kumburin nono
Yawan Jin Gajiya: idan kina fuskantar yawan jin gajiya bayan hakan bai saba faruwa ba yana daya daga cikin alamu.
Jirin Kai: idan kina yawan jin jirin Kai ba tare da wani da wani dalili mai ƙarfi ba, akwai alamun kina ɗauke da juna biyu.
Yawan Fitsari: haka ma shi yawan yin fitsari, idan kina yawan yin fitsari wanda kuma baki saba yi miki haka ba akwai alamun daukar ciki.
Yawan Munanan Mafarkai: wasu matan dazarar ciki yashiga wasu matan sukan fara yin munanan mafarkai.
Yawan Tashin Zuciya: idan zuciyar ki yana yawan tashiwa wanda kuma bai saba miki haka ba, akwai alamun kina ɗauke da ciki
Yawan Ciwon Ciki: yawan jin haka ba tare da da dalili ba zai iya kasancewa kin harbu da ciki.
Canjin Dandano: Da yawa daga cikin mata sukan fuskanci rashin jin daɗin dandanon bakin su ko na abinci.
Mura: wasu daga cikin matan mura tana zama a yayin shigar cik. hanci yakan iya yatoshewa , wasu hade da yawan yin tari. Musamman idan hakan bai saba miki haka ba.
- Karanta: alamomin ciwon ulcer
Wasu daga cikin alamun sun haɗa da:
- Yawan yin gyatsa
- Yawan Shah Ruwa
- Yawan Yin Tsaki
- Qin Cin Abinci
- Ciwon hanci
- Kurajen Fuska
- Yawan Zargi Ko Kokwanto
- Kaikayin Jiki
- Kumburin Hanci
Kowanne daga cikin misalai da muka ambata a sama, babu shakka sukan iya kasancewa alamomin ciki ne, sai dai kuma a wasu lokutan suna iya kasancewa akasin haka Saboda wasu dalilai na bambance-bambancen halitta.
Matan Kannywood da suka fi dukiya
Kina So Ki Tabbatar Da Cewa Kina Dauke Da Ciki?
Idan kina fuskantar wasu daga cikin alamun da muka gabatar a sama babu shakka zai iya kasancewa kina ɗauke da juna biyu. Amma ta yaya zaki kara tabbatar da haka? Domin tabbatar da cewa, zahiri kina ɗauke da ciki shi ne kaɗai ta hanyar ganin likita. Za’a iya mana a comment.