Alhaji Aliko Dangote har yanzu dai shine wanda ya fi kowa kudi a Afrika. Kuma shi ne wanda ya fi kowa kudi a kasar sa Nigeria, da tazara mai yawan gaske. Shine shugaban babban kamfanin kera siminti a Afirka wanda babu kamar sa, wanda aka fi sani da ‘Dangote Cement’. Alhaji Aliko Dangote shi ya mallaki kashi 85% na kamfanin mai suna Dangote. Kamfanin Dangote ya fara ne a matsayin karamin kasuwanci, sa’annan ya gina ta kamin ya zama yadda yake a yau.
Ana iya samun kamfanonin Alhaji Alinko Dangote a ƙasashe daban daban a yankin Afrika, kasashe da suka haɗa da; Ghana, Jamhuriyar Benin, Togo da kasar Kamaru, inda a kasar Kamaru kamfanin Dangote shi ne babban kamfani da babu kamar sa a duk fadin kasar Kamaru, kamfanin nasa yana nan ne a yankin tsakiyar birnin Douala Cameroun, a hanyar zuwa Bonabéri, kuma Douala shine cibiyar Kasuwancin kasar Kamaru,
Jerin Sunayen Mutanen Da Suka Fi Dukiya A Nigeria:
1. Aliko Dangote $13.7 billion
2. Mike Adenuga $6.5 billion
3. Alafaa Kariboye-Igbo $6.1 billion
4. Abdulsamad Rabiu $5.9 billion
5. Arthur Eze $5.8 billion
6. Cletus Ibeto $3.8 billion
7. Orji Uzor Kalu $3.2 billion
8. Emeka Offor $2.9 billion
9. Benedict Peters $2.7 billion
10. Andy Uba $2.1 billion
11. ABC Orjiako $1.2 billion
12. Leo Stan Ekeh $1.2 billion
13. Femi Otedola $1.1 billion
14. Danjuma Theophilus $1.1 billion
15. Jimoh Ibrahim $1.1 billion
16. Pascal Gabriel Dozie $1 billion
17. Folorunsho Alakija $1 billion
18. Igho Sanomi $1 billion
19. Jim Ovia $980 million
20. Tony Elumelu $700 million
MUTANEN DA SUKA FI DUKIYA A AFRIKA
Wanda Ya Fi Kudi tsakanin Naziru Da Rara