Sanatoci 5 Mafi Kankantan Shekaru Dake Kan Mulki A Nigeria
Nigeria kasa ce mai girma da kuma yawan al’umma ba zai zama mamaki sosai ba idan aka samu yan siyasa wadanda suke masu Kananan shekaru a cikin masu muƙamin gwamnati,
Amma kuma duk da kasancewar Majalisar dattawan na Najeriya wadda akwai wasun da suke da kanana shekaru acikin su da yawa, amma kuma akwai yan majalisar da suke shekarunsu sun ja acikin majalisar.
Sanatoci 5 Mafi Kankantan Shekaru Dake Kan Mulki A Nigeria
5. Ajibola Bashiru : 48
Ajibola Bashiru wanda aka fi saninsa da suna: ‘SRJ’ yanzu haka shine Sanatan a karkashin jam’iyyar APC, shine mai wakiltar jihar Osun ta tsakiya a majalisar dattawa. Kuma Ajibola shine Senior Advocate of Nigeria SAN. Ajibola shine shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai da al’umma a jihar.
4. Godiya Akwashiki: 47
Godiya Akwashiki; a yanzu haka shine Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a jihar Nassarawa. Kuma kafin zabensa a matsayin Sanata Akwashiki dama ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar PDP. Inda yayi Jagoranci daga shekarar 2011 zuwa 2015. inda kuma daga baya Akwashiki ya zama a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisa, dagaa shekarar 2015 zuwa 2019.
3. Bassey Albert: 47
Bassey Albert; shi ke wakiltar Akwa-ibom ta yankin Arewa maso Gabas na jihar Akwa-ibom a karkashin jam’iyyar PDP. an zabe shi ne a matsayin Sanatan yankin Akwa-ibom ta arewa tun a shekarar dubu biyu da goma sha biyar (2015). Sa’annan kuma a shekarar dubu biyu da goma sha tara (2019) ya sake lashe zabe a matsayin Sanatan yankin Akwa-ibom ta arewa a karkashin jam’iyyar PDP, a lokacinda aka zabe shi a shekarar dubu biyu da goma biyar lokacin yana da shekara 42 a duniya.
2. Yakubu Oseni: 45
Sanata Yakubu Oseni; yanzu haka shine dan majalisar dake wakiltan jihar Kogi ta yankin tsakiya a majalisar dattawar jihar karkashin jam’iyyar APC. Kuma ya taba zama a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin haraji a cikin jihar sa ta kogi. Shine na biyu a jerin mu na sanatoci masu Kananan shekaru dake kan mulki a yanzu haka.
1. Elisha Abbo, SIA: 42
Sanata Cliff Elisha Abbo wadda ake masa lakabi da SIA, wanda a shekarar dubu biyu da ashirin da biyu (2022) yan jihar sa na Adamawa suka masa sabon lakabi da “Babalade” kuma shi ne Sanata mafi karancin shekaru a fadin Najeriya inda shekarar sa arba’in da biyu ne kawai (42). An zabe shi ne a matsayin Sanatan Adamawa ta yankin Arewa a shekarar dubu biyu da goma sha tara 2019, a karkashin jam’iyyar PDP. Inda daga baya ya sake sauya sheka zuwa jami’ar APC bayan da ya samu masala da Gwamnan jihar wato Alhaji Umaru Fintiri. Inda kuma jam’iyyar APC a satin da ya gabata suka cire sa a matsayin dan takarar sanata.
“A ranar 7 ga watan Oktoban 2022 ne shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa ya amince da korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya bayar”.
Kotu ta kori Elisha Abbo a matsayin dan takarar ta